Buhari ya bada umarnin tsaurara tsaro a hanyoyin jirgin ƙasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar sufuri da jami’an tsaro da su tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a hanyoyin jirgin kasa.
Shugaban ya ba da umarnin ne a wajen rufe taron bibiyar ayyukan ministoci na 2022 da aka yi a yau Talata a Abuja.
Ya ce wannan umarni ta zama wajibi bisa la’akari da dumbin kudaden da aka narka a fannin sufurin jiragen kasa da kuma bukatar kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Ya ce: “Dole ne mu tabbatar da tsaron masu amfani da layin dogo kuma mu yi kokarin cimma burin tattalin arzikin da aka sa a gaba. Dole ne a lokaci guda mu tabbatar da jadawalin da za a iya tabbatarwa da kuma kula da matakin farko.
“Bayan nasarorin da aka samu a fannin tituna, tare da sabbin hanyoyin samar da da ababen more rayuwa, an umurci ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tattara jerin sunayen dukkan hanyoyin da aka kammala, gadoji da sauran ababen more rayuwa da za a fara aiki kafin karshen wannan gwamnatin. .''
Shugaban ya kuma ba da umarnin saka hannun jarin Gwamnatin Tarayya wajen sake gina wasu zababbun hanyoyin gwamnatin tarayya guda 21 da ke kan gaɓa wanda ya kai kilomita 1,804.6.
managarciya