Ku Daina Karba  Tsoffin Kudi CBN Ya Umarci ’Yan Najeriya 

Ku Daina Karba  Tsoffin Kudi CBN Ya Umarci ’Yan Najeriya 
Ku Daina Karba Idan Bankuna Suka Baku Tsoffi Naira, CBN Ya Umarci ’Yan Najeriya | Hoto: David Darius Asali: Getty Images Read more: https://hausa.legit.ng/news/1515437-ku-daina-karba-idan-bankuna-suka-baku-tsoffi-naira-cbn-ya-umarci-yan-najeriya/

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina  karbar tsoffin kudade daga bankunan kasar nan, RFI ta ruwaito. 

CBN ya ce wannan mataki ya zama dole domin kuwa wa’adin da ya debar kowa ya mayar da tsoffin kudin banki ya kusa zuwa karshe. 
Idan baku manta ba, CBN ya ce za a daina amfani da tsoffin kudaden N200, N500 da N1,000 daga ranar 31 ga watan Janairun bana bayan buga sabbi.
Da take magana yayin wayar da kan jama’a game da sabbin kudaden kasar da kuma mayar da tsoffi banki a birnin Lokoja, Mataimakiyar Daraktan Sarrafa kudaden Bankin, Dr. Rekiyat Yusuf ta ce akwai bukatar mutane su dauki mataki 
A bangare guda, ta ce CBN ya tanadi hanyoyi masu tsauri don ladabtar da bakunan kasuwancin da ke ci gaba da ba da tsoffi kudade. 
Game da matakin da mutane za su dauka, CBN ya ce ‘yan kasa za su iya kai korafin bankin da suka gani yana ba da tsoffin kudade a kan na’urar ATM. A cewarta, babu wani dalili da zai sa bankuna su ke ci gaba da ba da tsoffin kudade a daidai lokacin da suke da’awar daina karbarsu daga kwastomomin.
Daraktar ta kuma yi karin haske da cewa, an dauko kudurin sauya wasu daga kudaden Najeriya ne domin dakile aukuwar ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashawa a kasar. 
Hakazalika, ta ce sauyin kudin zai farfado da tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin kayayyaki da ake gani a yanzu. 
Wani rahoton The Guardian ya ce, har yanzu bankunan na ci gaba da ba da tsoffin kudade ga 'yan Najeriya. 
CBN ya ce akwai sabbin kudade a kasa, bankuna sun ki zuwa su dauka har yanzu, amma za ta dauki mataki.