Gwamnatin Zamfara ta ceto dalibban makarantar Bakura 18 dake hannun masu Garkuwa

Gwamnatin Zamfara ta ceto dalibban makarantar Bakura 18 dake hannun masu Garkuwa
Gwamnatin Zamfara ta ceto dalibban makarantar Bakura 18 dake hannun masu Garkuwa

Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin  Bello Muhammad Matawallen Maradun ta ceto dalibban makaratar Bakura 18 dake hannun masu garkuwa da mutane da suka sace a wani samame a satin da yagabata.
 
Gwamnati ta yi nasarar karbo yaran 18 dalibban makarantar Bakura a hannun masu garkuwar, a cikinsu mata 3 ne sauran maza ne.

 Gwamnan  Zamfara,  Bello Muhammad  ya nuna matukar jin dadinsa da wannan nasarar da gwamnatinsa take cigaba da samu. Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da aiki tukuru domin ganin ta kare rayukka da dukiyoyin Al'ummar jahar. 
 
Wadanda aka ceton sun nuna farincikinsu ga abin da gwamnati ta yi masu na ceto su duk da sun sha wahala a hannun maharan.