Matan da ke amfani da man gayaran gashi na 'relaxer' ka iya kamuwa da kansar mahaifa

Wani sabon bincike da masu bincike a kasar Amurka suka gudanar ya bayyana cewa matan da ke amfani da man gyaran gashi na 'relaxer' mai sinadarai masu karfi ka iya kamuwa da cutar kansar mahaifa.
Ciwon daji na mahaifa, nau'in ciwon daji ne da ke tasowa daga tantanin mahaifa.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa binciken da masanan a cibiyar kula da lafiya ta kasar su ka gudanar, ya hada da mata 33,497 na Amurka masu shekaru 35 zuwa 74, wadanda aka sa ido a kai kusan shekaru 11.
Kimanin kashi 60 cikin 100 na mahalarta taron da suka bayar da rahoton yin amfani da nau'in man a cikin shekarar da ta gabata, mata ne baƙar fata da suka gabatar da kansu.
Masu binciken sun ce a tsawon lokacin da aka gudanar da binciken, an gano cutar kansar mahaifa guda 378 a tsakanin matan.
Sun gano cewa matan da suka ba da rahoton yawan amfani da man gyaran gashi (fiye da sau hudu a cikin shekarar da ta gabata) sun ninka sau biyu fiye da yiwuwar kamuwa da cutar kansar mahaifa, idan aka kwatanta da wadanda ba sa amfani da man.
Binciken ya kara da cewa illar lafiyar kayan gyaran gashi na iya zama mafi girma ga mata bakar fata saboda su suka fi yawan amfani da su.