Bayan Kashe Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Matan Neja 26 da Suka Sace Sun Faɗi Buƙatarsu

Bayan Kashe Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Matan Neja 26 da Suka Sace Sun Faɗi Buƙatarsu



Yan bindiga sun saki wani bidiyo mai sosa zuciya na mata kusan 26 da suka sace a garin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.
A cikin bidiyon, matan sun roki 'yan uwa da abokan arzikinsu da su taimaka su kawo babura 130 da 'yan bindigar suka bukata domin a sake su. 
A cikin wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta samu, an ga daya daga cikin matan da aka sace daure a jikin bishiya tana fadin bukatun 'yan bindigar. 
Matar wadda ta yi magana da harshen Hausa, ta roki wani dan uwanta mai suna Abdulrahman da ya taimaka ya kawo baburan da aka bukata.
 "Umar, don Allah ka yi wa Abdulrahman magana. Sun kawo ni wani waje yanzu, sun ce ba za su sake ni ba sai an kawo abubuwan da suke bukata."
 A cewar matar, "Na samu rauni a kafa, sun ce in yi magana ta yadda za ku ji muryata kuma ku shaida ni. Na samu rauni a kafafuwana. Don girman Allah da ma'aiki, ku kawo kayan.