Bayan Ba da Hakuri, Tinubu Ya Kara Daukan Matakin Dakile Zanga Zangar Matasa

Bayan Ba da Hakuri, Tinubu Ya Kara Daukan Matakin Dakile Zanga Zangar Matasa

Gwamnatin tarayya ta kara daukan mataki domin ganin matasa ba su fita zanga zanga ba. Rahotanni sun nuna cewa sakataren gwamnatin tarayya ne ya fito da sabuwar hanyar da gwamnatin za ta nemi mafita a cikinta.

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yau Laraba ake sa ran yan majalisar zartarwa za su zauna domin tattaunawa kan zanga zangar. 
A karon farko, shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga matasa kan cewa su hakura da zanga zangar da suke shirin yi. A jiya Talata ne Bola Tinubu ya yi kira ga matasan kan cewa su jira su ga matakin da zai dauka kan matsalolin da suka ambata. 
Bayan kiran da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi, sakataren gwamnatin tarayya zai tara dukkan yan majalisar zartarwa domin daukan mataki na gaba. 
Rahotanni sun nuna cewa a yau Laraba, 24 ga watan Yuli dukkan ministocin za su zauna a ofishin sakataren gwamnatin tarayya. 
Haka zalika sanarwar ta nuna cewa wajibi ne ga dukkansu su halarci zaman da misalin karfe 10 na safe. 
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da matasa ke shirin zanga-zanga a wata mai kamawa, Ali Ndume ya bai wa shugaban Bola Tinubu mafita. Sanata Ndume mai wakiltar Kudancin Borno ya bukaci Tinubu ya kira masu shirya zanga-zangar su zauna a teburin sulhu da gwamnati. Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.