'Yan Bindiga Sun Saka  Harajin N200m Kan Wasu Kauyuka a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Saka  Harajin N200m Kan Wasu Kauyuka a Zamfara


Ƴan bindiga sun saka harajin kusan N200m kan wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara. Galibin ƙauyukan da abin ya shafa su na kusa da garin Kaura Namoda-Moriki a ƙaramar hukumar Zurmi. 
Jaridar Daily Trust ta ce ƙauyukan da abin ya shafa da harajin da za su bayar sun haɗa da Yan Dolen Kaura (N15m), Gidan Zagi (N15m), Kanwa (N20m), Kaiwa Lamba (N26m). 
Sauran sun haɗa da Gidan Dan Zara (N22m), Jinkirawa (N16m), Dumfawa (N16m), Ruguje (N7m), Babani (N3m) da Gidan Duwa (N4m). Mazauna ƙauyukan sun ce suna fuskantar matsin lamba kan su tara waɗannan kuɗaɗen cikin wani kayyadadden lokaci. 
An tattaro cewa tuni wasu ƙauyukan suka biya kuɗaɗen harajin nasu, yayin da wasu kuma ke ta fafutuka domin tattara kuɗaɗen da ake buƙata. Wani mazaunin garin Zurmi mai suna Malam Yunusa Musa ya shaidawa jaridar cewa harajin zai fara aiki daga wannan makon. "Abin takaicin shi ne mazauna garin Turawa sun biya N15m amma ƴan bindigan ba su sako mutanensu ba. Kauyuka da dama waɗanda harajin su yake tsakanin N26m zuwa N3m tuni sun biya kuɗin."