Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya nada masu bashi shawara sama da 10 a wata takarda da masu kula da harkokin yada labaransa suka fitar a kafofin sada zumunta a ranar Litinin data gabata.
Kwana daya da fitar da bayanin sai ga wata takarda ita ma da aka alakanta da daya daga cikin wadan da sunansa ya fito takardar Tambuwal, yana bayanin rashin karbar mukamin na mai baiwa gwamna shawara da aka ba shi a gwamnatin Sakkwato.
Usman S.K Danmajen Kebbe ya bayyana a takardarsa da ke yawo ma'aikacin gwamnati ne kamar yadda adireshin takardar ya nuna a hukumar tattara kudin shiga ta kasa reshen Lagos yake a yanzu.
Haka ya bayyana ganin sunansa a jerin mutane kamar kowa don haka ya yi godiya da karimcin da aka yi masa amma mukami a kai kasuwa.
A takardar ya dogara ga Allah a hukuncin da ya yanke, sai dai takardar ba ta da sa hannunsa.
Managarciya ta yi kokarin samun Danmajen domin samun cikakken bayanin kin karbar mukamin da ya yi, sai dai ba a samu nasara ba kan haka.
Wasu na ganin ya ki karbar mukamin ne domin ba wata hulda tsakaninsu da Gwamna Tambuwal, wadanda suka sanya a bashi mukamin ba su tuntube shi ba kafin mika sunansa.
Wasu na ganin ai shi tun da ma'aikacin gwamnati ne yana ganin irin wannan mukamin a farkon gwamnati yakamata a ba shi ba sai yanzu da aka kare tafiyar ba, ana maganar daura sabuwa.
Wasu na ganin harkokin da yake yi a Lagos sun fi ya karbi wannan mukamin ya dawo Sakkwato ya zauna yana budar baki.