Bala Kokani Ne Ɗan Majalisar Da Muka Fi Amfana Da Waƙilcinsa----Mutanen Tambuwal Da Kebbe
Wadanda yake wakiltar sun yi wannan furucin ne a wurin gabatar da tallafin da ya rabawa mutane masu karamin karfi domin su yi dogaro da kai, an yi bukin a garin Tambuwal a wannan satin. Dan majalisar tarayya dake wakiltar kananan hukumomin na jihar Sakkwato Alhaji Bala Kokani ya tallafawa mutanen mazabarsa da kudi domin su gudanar da sana’o’i. Ya rabawa mutum dubu mata da maza tallafin dubu 20 kowanensu, a wurin bayar da tallafin dan majalisar ya ce tallafin nada manufar samar da jari domin gudanar sana’ar dogaro da kai ga mutanen mazabarsa.
Mutanen Kananan hukumomin Tambuwal da Kebbe sun yabawa wakilcin dan majalisar tarayya Honarabul Bala Kokani kan wakilcin da yake masu a zauren majalisa domin suna amfana da romon dimukuradiyya.
Wadanda yake wakiltar sun yi wannan furucin ne a wurin gabatar da tallafin da ya rabawa mutane masu karamin karfi domin su yi dogaro da kai, an yi bukin a garin Tambuwal a wannan satin.
Dan majalisar tarayya dake wakiltar kananan hukumomin na jihar Sakkwato Alhaji Bala Kokani ya tallafawa mutanen mazabarsa da kudi domin su gudanar da sana’o’i.
Ya rabawa mutum 1000 mata da maza tallafin dubu 20 kowanensu, a wurin bayar da tallafin dan majalisar ya ce tallafin nada manufar samar da jari domin gudanar sana’ar dogaro da kai ga mutanen mazabarsa.
Ya ce an fito da shiraruwa domin amfanar mutane da yawa, ‘za mu baiwa mutane 400 teloli, manoma za mu raba musu babbar mota uku ta takin zamani da injimin ban ruwa 300 da injimin nika 200 da Babura kirar Bajaj guda 100 injimin heshin maganin haki 200, sai maganin kashin haki mai yawa domin rabawa manoman rani a yankina da gero mai yawa don rabawa masu karamin karfi’, a cewar Bala Kokani.
Ibada Balarabe daya daga cikin wadanda suka samu tallafin ta yi godiya kan tallafin da ta samu, ta ce a tun sanda ake wakilci a yankin ba su samu gajiyar dimukuradiyya kamar wannan lokacin ba.
Larai Muhammad Labaran ta ce wannan kokarin nasa abin yabawa ne domin za mu iya dogaro da kanmu ga wadan nan kudade, hasalima ba a taba yi mana haka ba sai a wannan lokaci na wakilcin Bala Kokani.
Muhammad Yawaya ya ce wannan abin yabawa ne Bala yana yi mana abin da tsoffin ‘yan majalisarmu biyu suka kasa yi mana, a yanda yake kula da jamarsa gaskiya sai sambarka.
managarciya