Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sha Alwashin Cika Alƙawullan Da Ya Ɗauka Kafin Ƙarshen Wa'adinsa

Hon Kabir Ibrahim Tukura ya yi kira ga al'ummar zuru, Fakai, Danko wasagu, da Sakaba, da su, cigaba da ba gwamnati, jiha da ta tarayya, cikakken hadin kai, da goyon baya, domin ta cigaba, da samar, masu da ababen more rayuwa.  A cewarsa lokaci ya yi da al'umma za su, ci moriyar dimokradiyya fiye da kowanne lokaci. 

Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sha Alwashin Cika Alƙawullan Da Ya Ɗauka Kafin Ƙarshen Wa'adinsa

Daga Abbakar Aleeyu Anache, 

Ɗan Majalisar wakilan tarayya Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin zuru, Fakai, Danko wasagu, da Sakaba, dake jihar kebbi, ya bayyana farin ciki bisa goyon baya da addu'o''in da al'ummar zuru, suke baiwa gwamnatin jihar kebbi dama kasa baki daya, ya ba da tabbacin yin duk abin da ya kamata wajen kare muradun su a kowanne, mataki.

Hon Kabir Ibrahim Tukura ya yi kira ga al'ummar zuru, Fakai, Danko wasagu, da Sakaba, da su, cigaba da ba gwamnati, jiha da ta tarayya, cikakken hadin kai, da goyon baya, domin ta cigaba, da samar, masu da ababen more rayuwa. 

A cewarsa lokaci ya yi da al'umma za su, ci moriyar dimokradiyya fiye da kowanne lokaci. 

Ya ba da tabbacin cika alƙawullan da ya ɗauka kafin wa'adinsa ya zo ƙarshe.