Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya jagoranci wakilan jam’iyyar sun sa labule da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta ranar Asabar.
Sauran tawagar wakilan sun haɗa da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa a PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.
Mai taimakawa tsohon shugaban kasa kan harkokin watsa labarai ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar sakamakon rashin sanin yan jarida gabanin fara taron.
A cewar sanarwa, taron wanda ya gudana a sirrance ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyintola, tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da kuma d’an kasuwa, Oyewole Fasawe
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa: “Sako na ga ‘yan Najeriya shi ne su fito kwansu da kwarkwata idan ranar zabe ta zo a watan Fabrairu su dangwalawa tikitin da ya hada yan takarar da suka yi dai-dai da al’adar kasar nan, wadanda zasu kafa gwamnatin da zata hada kan kasa.”






