Shugaban Majalisar Dattawa Yayi Jajen Mutuwar Sanata Joseph Wayas

Shugaban Majalisar Dattawa Yayi Jajen Mutuwar Sanata Joseph Wayas
Shugaban Majalisar Dattawa Yayi Jajen Mutuwar Sanata Joseph Wayas 
Daga Babangida Bisallah
Shugaban majalisa dattawa, Ahmad Lawan ya aike da sakon jajen sa ga iyalan tsohon shugaban majalisar, Joseph Wayas wanda ya rasu a ranar Alhamis. 
Bayanin sakon na kunshe a takardar manema labarai da mai ba shugaban majalisar dattawa shawara a aikin jaruda Ola Awoniyi ya sanyawa hannu.
Ya cigaba da cewar Lawan ya jajanta ma iyalan tsohon Sanatan, gwamnati da jama'ar jihar Cross River da abokan mamacin. 
Ya bayyana mutuwar Sanata Wayas a matsayin wani babban rashi ga Najeriya. 
Yace, "Sanata Wayas ya kasance wani kwararren dan majalisa kuma shugaba na siyasa wanda ya bauta ma kasar sa da jama'a cikin sadaukar wa da rikon amana. 
"A matsayin sa na shugaban majalisar dattawa, Sanata Wayas ya jagoranci majalisar da kwarewa da karsashin aiki. Ya kasance wata babbar alama na siyasar zamanin sa. 
"Ko bayan barin aikin sa a 1983, Sanata Wayas yaci gaba da bada gudummuwa wajen gina kasa, dimokaradiyya, da tattalin arziki da zamantakewar jama'a. 
"Ya taka muhimmiyar rawa a matsayin sa na mataimakin shugaban taron sake fasalin kundin tsarin mulki a 1994 zuwa 1995, baya ga wasu ayyukan raya kasa da ya bada gudummuwa . 
"Tabbas, Najeriya zata yi rashin dimbin kwarewar sa." 
Shugaban majalisar yayi addu'ar Allah ya ba dangin sa hakurin jure wannan rashin.