NNPP Ta Dakatar Da  Shugabanta Da Wasu Mutum Uku Kan Yiwa Jam'iya Zagon Kasa a Sakkwato

NNPP Ta Dakatar Da  Shugabanta Da Wasu Mutum Uku Kan Yiwa Jam'iya Zagon Kasa a Sakkwato

 

Jam'iyar adawa ta NNPP ta kori mukaddashin shugabanta na jihar Sakkwato Injiniya Bello Ahmad tare da wasu mutum uku kan zargin da ake yi masu na yiwa jam'iyar zagon kasa da yin jagorancin mutum daya a jihar Sakkwato.

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyar a jiha Mustafa Sani Tangaza ne ya sanarwa manema labarai matakin da aka dauka bayan kammala zaman majalisar zartawar jam'iyar a wannan Talatar.
Ya ce sun yi matsayar korar mutum hudu a jam'iyar "tsohon shugaba Injiniya Bello Ahmad da mataimakin shugaba na Sakkwato ta tsakiya Ahmad Isa da mataimakin Sakatare Abdullahi Da'a da kuma Murtala Sani shugaban matasa na Sakkwato ta tsakiya, dukansu mun dakatar da su kuma su kadai ne, duk wanda za su yi huldar siyasa da shi kashin kansu ne ba madadin NNPP ba," a cewarsa.
Mustafa ya ci gaba da cewa ba za su yi tafiya ga duk wanda ba ya da gaskiya ga lamarinsa, 'kafin aiwatar da wannan matakin mun sanar da uwar jam'iya duk abin da muke yi muna biyar doka a cikin tafiyarmu.
'Bayan sallamar shugaban an amince da nada mukaddashin shugaba Abdurra'uf Yusuf Kyadawa kafin wannan nadin shi ne mataimakin shugaba a yankin Sakkwato ta gabas. 
'Wannan shugabanci zai kawar da sanyin guiwar da wasu ke yi a cikin tafiyarmu, muna kira ga shugaba ya jure ya jajirce don samun nasara, ya zama da zuciya sakakka da kawarda wautar mutane don ciyar da jihar Sakkwato gaba,' in ji shi. 
Sabon mukaddashin shugaban Abdurra'uf Kyadawa a jawabinsa na amincewa ya ce manufarsu kawowa Sakkwato zaman lafiya da gina matasa da mata da dawo da aikin gwamnati cikin haiyacinsa, za su samar da kyakkyawan jagoranci a jam'iyarsu.  
Duk yunkurin jin ta bakin tsohon shugaban da aka dakatar da sauran mutum uku hakar ba ta cimma ruwa ba.