Akwai Yiwuwar Atiku Zai Yi Aiki Da Kwankwaso Da Obi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Akwai Yiwuwar Atiku Zai Yi Aiki Da Kwankwaso Da Obi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

 

Atiku Abubakar mai neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP, yana tunanin kafa gwamnatin hadaka a Najeriya. Jaridar This Day tace Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar da kan shi bayan ya gama zantawa da gungun mutane a Kano.

‘Dan takaran na jam’iyyar PDP yace gwamnatinsa za ta tafi da kowa a Najeriya domin ganin an hada-kan al’ummar kasa, tare da magance matsalar tsaro. 
A ganin Atiku, tafiya da kowane bangare a cikin gwamnatinsa, zai rage zafin sabani a Najeriya.
“Akwai batun la’akari da kafa gwamnatin hadin-kai da zai rage zafin rabuwar kai, ya hada-kan ‘yan Najeriya.
Kuma ya kawo ingantar halin tsaro. Idan aka samu tsaro, kudi za su shigo, saboda haka tattalin arziki zai bunkasa.” 
Da yake jawabi a ranar Talata, mai neman kujerar shugaban kasar ya dauki lokaci yana tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar tattalin arzikin kasa. 
Wazirin Adamawa yace idan aka samar da tsaro, tattalin arziki zai bunkasa ta hanyar tatsar haraji da kyau, da kuma jawo masu hannun jari daga kasashen waje. 
Rahoton Premium Times yace Atiku ya soki yawan bashin da gwamnatin Muhammadu Buhari take ciki, yace ana boye gaskiyar halin da kasa take ciki.