Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Ambasada Faruk Malami Yabo ya bayyana ficewa daga jam’iyyar tare da shiga PDP ta su gwamna mai ci a jihar, Aminu Waziri Tambuwal.
Ambasada Yabo, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jordan da Iraqi ya bayyana shiga PDP ne a lokacin da tawagar kamfen din PDP ta dira karamar hukumar Yabo a Laraba 4 ga watan Janairu.
Ya bayyana shigarsa PDP a matsayin dawowa gida, inda ya ce jinin PDP ne ke yawo a jikinsa, wacce ke mulkin jihar a Arewa maso Yammacin Najeriya, a farko sun ga alherin PDP wanda suke fatan sake gani a gaba.
“Sauya shekar daidai take da mutum ya dawo gida, Ina goodiya ga kowa da ke cikin wannan tafiya kuma na yi alkawarin taimawa jam’iyyar don ta yi nasara a zabe mai zuwa a jihar.”
Managarciya ta tattaro cewa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne ya karbi Yabo zuwa PDP, kuma ya yaba masa da gano gaskiya.
A cewar gwamnan, shigowa Yabo PDP ya sanya ranar ta jiya a matsayin rana mai cike da tarihi ga siyasa da dimokradiyya a jihar Sokoto.
Tambuwal na cewa: “Dan uwa, bayyanawarka a hukunce ka dawo PDP, babban ci gaba ne a aikin da ke gabanmu.
“Wannan na ci gaba da nuna haske ga PDP cewa za ta yi nasara a jihar Sokoto da ma Najeriya baki daya, na samu gamsuwa sosai muna da nasara.”





