Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya rantsar da Manyan Alkalan Babar Kotun Jiha 5 da Khadi biyu a zauren fadar gwamnatin jiha a wannan jumu'ar.
Tambuwal ya rantsar da su ne kamar yadda doka ta ba shi dama domin aiwatar da aiyukkan kotuna daban-daban a fanin shari'a a jihar.
Alkan da aka rantsar hudu maza da mace daya Sanusi Shehi Esq da Prof. Muawiya Dahiru Mahmud Esq da Abubakar Abubakar Zaki Esq da Mohammed Aliyu Sambo Esq da Maryam Muhammad Esq.
Bayan nan kuma ya rantsar da Khadi su biyu Buhari Yahaya da Dakta Umar Jibril Kebbe.