MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita ta 26,27

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita ta 26,27

Page 26____27

 

 

 

Cikin sauri suka nufi  ɗakin Huraira banda addu'ar Allah yasa burinsa ya cika babu abin da Malam Ummaru ke yi, yayin da shima a nashi ɓangaren malam Shehu mai Tawada fatansa marar lafiyar ta kasance irin tasa yanda zai ce akai masa ita gidansa yayi mata maganin acan.

 

 

Gaba ɗaya Huraira ta shiga cikin mayuwacin halin yin arbarta da wata mummunar halitta wadda tunda take gane-ganenta bata taɓa ganin irin wannan mummunar halittar ba, buɗe baki tayi da nufin kwartsa ihu sai ga wani ƙaton hannu yayi fitar burgu daga cikin bakin halittar ya nufi Huraira ya daɗe mata baki gum.

 

Wata narkekiyar halittace mai manyan kunnuwa sama da goma kanta guda ɗaya ne amma ya cika ɗakin ga wani irin idanuwa masu kama da idanun damisar dawa irin wadda ke jin yunwa taga nama, jikin kumatunta kuwa sun tsattsage wasu tabka-tabkan manyan tsutsoci na fitowa suna shigewa cikin bakinta tana taunewa, gaba ɗaya jikinta wani irin gashine marar kyan gani ta zazzalo harshenta waje wasu allurai sun fito saman halshen kamar an dasasu, haƙoranta wasu irin jajaye gasu da mugun tsini tamkar bakin mashi, madadin gashi ita kanta wasu tabka-tabkan manyan macizaine saman kan ƙaton kan nata sai motsi suke suna buɗe bakunansu, ga wasu  manyan hannuwa sun kai bakwai kowane da akafar da tayi tsayi na ban mamaki, cikin wata ƙatuwar murya ta dakama Huraira tsawa "Ubanwa yace ki ɓatamun aiki ? Sautin muryaita yasa Huraira sulalewa a sume gun ita kuma ta zama hayaƙi ta shine cikin jikin Huraira.

Nan take Huraira ta bingire a gun ta cigaba da sheƙa barci mai nauyi.

 

Malam mai Tawada shine kan gaba gun shiga ɗakin, musamman da ya ji tsit ko irin ɗan kururuwar nan bata yi sai yaji a ransa yau ko shakka zai samu ta sauyawa yau dan haka ya juyo ya kallesu yace "Ku dakata daga nan ni zan dubata kun san irin waɗan can shauɗanun basu san yawan mutane a gunsu dan Allah ku yi zamanku a can (ya nuna kofar ɗakinsu Bilkisu) kuyi ta addu'a kuna ƙarawa ni zan shiga nayi masu aikin gaggawa" ya shige cikin ɗakin hada su gyara labule, malam Umaru yayi kamar zai bishi cikin ɗakin, ai da sauri mai Tawada yace "A'a Malam koma can kaima dan aikin bana wasa bane ba. Shi kam malam Umaru banda dariya ƙasan ransa ba abin da yake, musamman da yaga sai wani zumuɗi yake dan haka yace "Wai da tare maka hanyar zan kada ta rugo kasan Aljanu da tsoron irinku ai " hakan yasa mai Tawada yace "Anyi haka fa, to ka ja mana ƙofar kada su ruga a rasa mai kamosu kam.

Cikin matuƙar farin ciki malam Umaru ya ja ƙofar ya rufe gam dasu rataya ɗan makullin dake jikin ƙofar, hakan yasa Bilkisu yin magana cikin alamar rashin yadda da abin da ke faruwa na rufe Inna tare da wani cikin ɗaki su kaɗai, malam Umaru ya dubeta ya ɓata rai sosai yace "Dan gidanku Bilkisu ke zaki gayama abin da ya kamata muyi ne ? To bari kiji gaskiyar magana ana fara mata ruƙiyya ta ɓalle ta ruga duk cikin anguwar nan ba mai iya kamota. Jin hakan yasa tai tsit ta shige ɗakinsu tana share hawaye kawai, Malam Umaru ya dubi bayanta yace "Kaga ja'irai yarinya na neman ta rusa mun duk wani bajat? Ya ciji leɓe ya sake gyara kwaɗon ya koma gun yaran Malam Shehu mai Tawada ya zauna yana addu'ar Allah yasa yau mai Tawada ya gane kurensa.

 

 

Cikin ɗaki kuwa Malam Shehu na shiga ya iske Inna Huraira sai sheƙa barci take ba wani alamar tana iya gane wanda ke kanta, yasa ya fara lashe baki yana jin yau ranar sace, tabbas zai samu abin da ya sama jikinta kafinta farka daga barcin nan, dan haka bai tsaya jiran komi ba ya isa gabanta ya tsugunna yana ƙare mata kallon ƙurulla irin wanda ko maye baima wanda yake hari kai tsaye, a hankali yasa hannunsa ya cire hannunta daya kare mata fuska, wani matsiyacin shauƙi ya ƙara kamasa ganinta fes da ita, kai tsaye tunano wani Indian film yayi wanda yaga wani tsoho kamarsa na sumbatar wata mace sai yaji abin ya burgesa so yake kawai ya gwada akan Huraira dake baje ƙasa sai barci take abunta.

 

 

Gaba ɗaya Barriratul Azam ta gama fusata da lamarin malamin domin a rayuwarta ta tsani tana jikin bil'adama azo ace za a bata umarni to tabbas sai ta jigata ko waye dan haka tai lub taga gudun ruwan Malam Shehu yau .

 

 

Shikam Malam Shehu a hankali ya tsugunna yana tuno Film ɗin yana murmushi ya nufi bakin Huraira da bakinsa wai shima kiss zai mata. Sai dai yana zuwa gab da bakin yaji wani matsiyacin zafi na fitowa daga fuskarta yana bugar fuskarsa kai tsaye wanda bai da maraba da zafin wuta, sai ya ɗago yana dubanta da alamar mamaki domin bai taɓa ganin inda kai ke fidda hucin zafi ba duk ciwon da yake yi sai yau, dan ya tabbatar sai ya taɓa jikinta nan kuma yaji sanyi ƙalau ba wani alamar zafi. Dariya ya kwashe da ita yana ganin ko shakka babu ita nata aljanun iyakar kanta suke dan haka ba ruwansa da wani kai yanzu, to ai daman jikin yafi kan daɗin lamari da sha'ani, dan haka ya miƙe tsaye ya cire rawaninsa ya cire rigar ya kwance wandonsa yana cewa a ransa, "kawai na afka nayi abin da zan yi tun kafin lokaci ya ƙaremun.

 

Huraira tayi wata uwar ƙara ta mike zaune tana zare idanuwa kamar na mujiya duk sun fito sunyi ƙuru-ƙuru sai wani hayaƙi ke fitowa daga cikinsu ba kyan gani bada ɗaya ta juye kamannin fuskarta zuwa na wata halitta da batai kama data mutane ba. Tunda tayi ihun nan jikin Malam Shehu ya ɗanyi sanyi domin bai taɓa samun mai lalurar da tayi ihu mai karfi da amsa amon wannan ihunba, amma da ya tuna abin da yake hari sai yaji ya samu damar da zai amfani da ita ya fake yayita ruƙunƙumeta har dai ya samu ya samu damar biyan buƙatarsa ai ɗan Hausa ba bagwari bane ba, ko da ya gama wannan tunanin bai jira komai ba ya daka tsalle ya afka jikinta wai karta gudu yana ihun cewa "Malam ku rufe ƙofar da kyau karta fito wannan nata matsiyatan mahaukata ne sai naci ubansu yau sai na ladabtar dasu na ƙone tsinannu ai sun haɗu da gamonsu yau ko ni ko su ai " shikam Malam Umaru ai sai ya ida datse ɗakin ya ruga gun yaran Malam Shehun yana kun gani gara dana rufesu ko ? Su dai jinsa kawai suke amma sun san halin Malamin nasu sarai bai da gemu ko kaɗan, Allah dai yasa ya gane ba kyau lalube matan mutane da ƴaƴan mutane ya daina kawai .

 

 

Ya dage iya karfinsa ya rumgumeta sai wani nishi yake mai nuna wata alamar ta alamar ya fara antayawa cikin shauƙi yaji wani baƙon lamari na ratsashi ta ko ina wanda bai san lokacin da ya fara ƙoƙarin kwace jikinsa daga gareta ba amma ina ya kasa kamar danko haka yaji jikinsa ya manne jikin matar, wani irin zafi ke fitowa daga jikinta yana ratsashi gashi tamkar ana tsira masa allura a cikin jikinsa haka yake ji bai san lokacin da ya fara kokowar tureta ba amma ba halin hakan dan gaba ɗaya ya kasa turetama dan haka ya ɗago ya kalli fuskarta, ai san sanda ya wage ƙaton bakinsa ba yana ihu "ku zo ku rabamu dan Allah na shigesu ni mai Tawada yau gani ga Aljana muna kokowar gaske .

 

A waje kuwa banda tashin karatun mai Tawada babu abin da ake ji wanda hakan yasa Malam Umaru ya fara jin haushi dan ba tantama yasan yasha tunda yake karatun can . Jin karatun yasa Bilkisu a natsuwa har itama ta fara jan carbinta tana lazumi.

 

 

Kallon yanda fuskarta ta koma kawai yake ashe aljana ce daman zaune a cikin gidan dan iskanci Malam Umaru ya kirasa ? Ji yayi ta ɗagashi sama ta wurgas kansa ya bugi bango, ta nunashi da ƙaramin yatsanta sai gashi wani kan maciji ya fito ya nufi inda yake kwance, ai bai san sanda ya yunƙura ya tashi ba ya nufi ƙofar ɗakin ba yana ihu ku buɗe karta kasheni dan Allah na tuba na biku " sai dai ga alama su muryai Huraira suke ji tana cewa "Sai mun kaita daji ko dawa kake taƙama yau Malam"  ai da gudu suka je suka rufe ƙofar shigowa gidan dan karma tsautsai yasa su balle ta ɗakin su yi wajen kamar yanda suke cewa.

 

Aljana Barriratul Azam ya kallesa ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya wadda iska ya fito ya haifar da ƙaramar guguwa a gun, sai ɗakin yayi uban duhu yanda ko hannunsa ya ɗaga bai iya ganin tafin hannunsa sam, ya ɗago kansa ya kalli inda yake tunanin Aljanar na gun yaga wasu irin idanuwa manya masu girma da faɗi guda uku kowane da irin kalarsa ba kyan gani, cikin duhun dai yake ganin yanda idanun ke jujjuyawa kamar majaujawa ido ɗaya hawayen jini yake fesowa tamkar yayyafin ruwan sama , ɗaya kuma wani baƙin ruwane mai kama da ruwan kwata yake bubbulowa ba ƙakkautawa, ɗayan kuwa yana iya gane yanda yake galla masa wata uwar harara kamar maƙiyi yayi arba da maƙiyinsa, ko kuma kishiya taga shigar kishiyarta ɗakin maigidansu.

Gaba ɗaya Malam mai Tawada ya ɗimauce, ya fara fita hayyacinsa, bai taɓa ganin bala'i da musiba irin wannan ba, kai shi duk tsawon lokacin da ya ɗauka yana iƙirarin cire Aljanu bai taɓa katari da irin wannan musibar ba, gaba ɗaya ya kasa karanto ko da kalma guda ce daga cikin ayoyin neman tsari sai mazari da karkarwa da jikinsa ke yi baki ɗaya.

 

Yana cikin wannan halin ne yaga ɗakin yana washewa haske ya bayyana yayi arba da wata gabjejiyar halitta wadda bai taɓa ganin irinta ba ko a cikin irin fina-finai na ban tsoro da yake gani da jin labari, da kansa yaji inama ya sume a gun, tabbas da ya huta da ganin wannan bala'i mai neman haukatar dashi, ahankali halittar ta fara rikiɗewa tana komawa suffar ƙaton dodon aljani wanda ke da ƙahunna uku a kai idanu uku hanci uku kunnuwansa uku ga wani baƙin jini dake fitowa daga idanunsa yana ziro halshe yana lashewa, gaba ɗaya jikinsa babu fata sai zallar naman kawai kake gani jawur ba kyan gani, bindinsa uku ɗaya a bayansa ɗaya a gabansa ɗaya a tsakiyar kansa bayan ƙahonsa na tsakiyar kai, jini sai zuba yake tamkar an yanka dabba amma jinin baƙi wuluk ne ba wani alamar ja a jikinsa. Cikin razana Malam Shehu ya runtse idonsa yana fatan daman ya sume aljanin ya ƙyalesa, sai jin wata zazzaƙar murya yayi tana kiran sunansa cikin salon soyayya da shauƙi. Buɗe ido yayi yaga daga ina wannan muryai ke fitowa yayi arba da wata kafceciyar mata gaban dodon, tana riƙe da bindinsa tana wani rausaya tana jujjuyawa kamar tarwaɗa, kallon fuskarta yayi yaga gaba ɗaya idonta guda ne kumatunta manya-manya hancinta ƙaton gaske amma a taɓe yake ba kyan gani, idonta ya sake kallo ya ganni kamar jan gauta, ga wani gashi da yayi cirko-cirko a tsakiyar kanta ba kyan gani sai wani hayaƙi ke fitowa daga cikinsa tamkar ana hura wuta cikinsa da ɗanyen icce.

Kawai ji yayi ta fisgosa ta manna da jikinta ta wankale bakinta da ba komi ciki illa manyan kunamu sun tada ƙarinsu sama, ihu ya zunduma yana neman taimakon a buɗe kofa karsu kasheshi sun ƙara yawa, amma a banza babu mai jinsa balle yasan mi yake faɗi ma.

 

Duk yanda yaso ya rufe bakinsa bai iyawa yana ji yana gani mummunar Aljanar nan ta haɗe bakinsu waje guda. Wani masifeffen  zafi ya dinga ziyarar ƙwalwarsa nan take yayi ihu ya sulale a sume bakinsa da fuskarsa sun kumbura sun haye kamar kwabin fanken kasuwa, cikin dariyar mugunta Aljana Barriratul Azam ta dubi ƙaton dodon kawai suka koma hayaƙi suka ɓace, ɗakin yayi duhu mai ban tsoro na ɗan wani lokaci, sai kuma ya washe sai gasu a suffar mutane mace da namiji ɗauke da manyan bulali kai tsaye suka fara zubama Malam Shehu ai kawai ganinsa yayi yana ihu yana kiran sunayen duk wanda Allah yasa ya faɗo masa azo a ceceshi.

Duk inda bulalar ta sauka take gun ke darewa ya tsage jini yayi tsartuwa, kafin kace me , Malam Shehu gaba ɗaya kamanninsa sun sauya ya koma kamar wani horo shima dan azabar duka da yake ci bana wasa ba, sai da kayansa baki ɗaya suka yage komi ya bayyana fili na jikinsa kana suka ɓace lokacin yayi doguwar suma shima.

 

A daidai lokacinne Babansu Bilkisu ya dawo yanata buga ƙofar gidan yana mamakin abin da yasa aka rufesa da rana haka, a cikin ransa yake tunanin ko lalurin Huraira yayi nisa ne yasa aka rufe ƙofar ? Yana cikin tunanin ne malam Umaru ya buɗe masa ƙofar yana shaida masa abin da suke jiyowa daga cikin ɗakin da ake ma Huraira magani. Tare suka jera suka isa cikin gidan kai tsaye Babansu Bilkisu ɗakin ya nufa ya buɗe ya shiga cikin ɗakin da sallama a baƙinsa, "Inna'ilaihirraji'un ! Kuna aikin me haka ta faru Malam Umaru ? Allah yasa batai kisan kai ba to" nan take cikin Malam Umaru ya yamutse jin an ambaci kisan kai, shifa ba kisan kai yake so aiba, so yake dai a koyama Malam Shehu hankali ne kawai sakamakon irin ayyukan da yake na zalunci da cin amana.

 

Jin maganar Babansu Bilkisu yayi yana cewa "Ku shigo man kugani ai abin bana wasa bane ba" da hanzari ya sungumi butar ruwa da yagani gabansa ya faɗa cikin ɗakin sauran yaran mai tawada suka mara masa baya hankali tashe.

Suna shiga Malam Umaru ya fara zuba masa ruwa ya ja wata irin ajiyar zuciya numfashinsa ya dawo amma ba baki sai binsu yake da ido kawai yana hawaye, cikin ransa banda tsinema Malam Umaru babu abin da yake yi domin shine munafikin daya kawosa inda aka so kasheshi, Allah kawai zai saka masa irin wannan azabar da aka yi masa yau, ko shakka babu sai ya saki yarinyar Malam Umaru yana komawa gida, saboda ubanta mugune azzalumi matsiyacin banza so yayi ya kaisa inda za a kasheshi ai ya gane nufinsa yanzu.

 

Bilkisu ce ta shigo tana tambayar ina Innarsu ? Sai a lokacin aka fara neman Huraira bata ba alamar ta a cikin ɗakin,kuka Bilkisu ta fashe da shi tana kiran sunan Innar tasu amma tsit bata amsa ba, hakan yasa Babansu ya leƙa ƙarƙashin gado sai gata male-male tana fidda numfashi da ƙyal, cikin sauri ya janyo ta yana mata sannu wanda ita kamar batama san abin da ke faruwa ba .

 

Ai Malam Shehu na ganin ta tashi zaune ya miƙe da gudun tsiya ya fice ɗakin yana cewa "Wallahi kuna tare da baƙar aljana kunga tafiya tani ba zan zauna ta ida kasheni ba" ai yaran nasa basu jira komi ba suka mara masa baya suna ihun "Gata nan Malam ƙara sauri " shi kanshi Malam Umaru lamarin ya bashi tsoro ainun domin yaga yanda kai tsaye aka sauyawa surukin nasa kamanni ga duk an fasa masa jiki da gani bulalace amma ba bulalar ga bakinsa da yaga yayi suntum kamar an gasa biredi .

 

Huraira kam sai kalle-kalle take kamar taci babu itama ga alama batasan miya faru a gunba, amma ganin maƙwabcinsu a ɗakinta sai ranta ya ɓaci duk da tsamin da fuskarta tayi bai hanata fara fara masifar "Miya kawoshi har cikin ɗakinta tasan dai ganin ƙwab ne ya kawosa to wlh ba da itaba wannan iskancin maza ya bar mata ɗaki kafin ta ɗauki mataki.

 

Ai daman neman hanyar fita yake dan kada malam Ahmed yaga rashin kyautawarsa yasa tuni bai cika wandonsa da iska ba daman da yanzu ya manta ya isa gida shi, dan haka ya miƙe ba bayanin komi ya fice ko ta kan takalmansa baibi ba .

 

Bilkisu gaba ɗaya ta gama ruɗewa kan lamarin Innar tasu abin nata yayi yawa dan haka ya kamata ayi bincike kan lamarin .

 

 

Daidai lokacin Yah Malam ya ɓace daga jikin bangon ɗakin yana jin ciwon yanda Bilkisu ke san ta tona masa asiri dan haka zai sauya wani takun mai ban mamaki da al'ajabi kan lamarin.

 

To komi zai faru kuma ?