BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
بسم الله الرحمن الرحيم
FITOWA TA SHA TAKWAS.
~~~Shi ma Baba haka ya bamu labarin rayuwar da suka yi shi da ɗan uwansa sannan ya ce "na tabbar da yanzu sun kashe min ɗan uwa".
"Inason na koma gida domin na duba wanne hali mahaifiya ta take ciki ita da ɗan ɗan uwana",ya iyar da maganar yana kallon Malam.
"Hakan yana kyau gaskiya domin na tabbata yanzu haka tana can tana tunanin a wane hali kake", malam ya faɗa yana me kallonmu.
"Kallonmu shima ya yi sannan ya ce "kuzo ƴaƴana kuzo naji ɗinmin jikinku, gaba ɗayanmu muka rankaya muka shige jikin mahaifinmu yana me shafa kawunan mu haɗi da sanyawa rayuwarmu albarka.
Miƙewa Malam ya yi ya fice daga ɗakin ya yinda Baba ya yi azamar miƙewa ya nufi gurinda Mama take zaune ya rungume ta, ganin hakan ya sanya ni jan ƙannena muka fita daga ɗakin.
Sosai Baba ya dinga yiwa Mama godiya , kana daga ƙarshe yace "mu shirya gaba ɗayanmu domin gobe muje gurin mahaifiyarsa."
Sosai muka ji daɗin hakan domin kuwa ko bakomai zamu ga mahaifiyar mahaifinmu.
Munga mutane da dama waƴanda ke shigowa domin tanya mu murna da kuma waƴanda tsegumi ne ke shigowa dasu duk sunzo.
★★★★★★
Jikin Hajiya Umma ya rikice sosai wanda hakan ya yi sanadiyar tashin hankalin ƴan gidan.
Ƙarfe 2pm suna tsatstsaye a bakin ɗakin da take ciki tare da likitoci suna duba jikinta , sosai su Safara'u ke kukan fitar rai, wanda hakan ya yi masifar ta dawa Alh Bello hankali.
Fitowar likitocin daga cikin ɗaki ne yasan yasu saurin isa gurin suna tambayar ya jikinta, kallo ɗaya ta yi masu kana ta ɗauke kanta haka kawai taji ba zata iya sanar dasu ba, sai Kawai ta nuna masu ɗakin da hannu.
Su dukansu suka ɗunguma suka faɗa ɗakin ganinta rufe ruf da farin zane ya sanya su jan birki nan hwa yara da manya akayita rafzar kuka.
Allahunta , Hajiya Umma an rigamu gidan gaskiya, Allah ya jiƙan magabatanmu.
Bayan anyi cike cike aka basu gawarta kai tsaye gida suka dawo, anan aka shiryata ƙarfe 5pm aka kaita gidanta na gaskiya, gidan da komai mulkin mutum dole saiya shigesa {Rabbu yasa muyi ƙarshe me kyau}
A haƙiƙanin gaskiya kowa mutuwar Hajiya Umma ta girgiza sa, kasan cewar ta mace wacce tasan yadda take zama da mutane akwai son yara haɗi da kyauta gana ƙasa da'ita.
Zaman makoki a kaci gaba dayi a gidan ya yinda da zaran kaga Alh Bello zaka tabbatar da baya cikin nutsuwarsa.
★★★★★★
Sai dare sannan na samu lokacin kunna wayata wacce gaba ɗaya yinin yau ban samu lokacin buɗe ta ba, ina kunnata kuwa mssg suka dinga rigengen shigowa , ina riƙe da ita ina jiran ta ɗanyi 2minutes sai ga kira ya shigo.
Sai da gabana ya faɗi na rasa dalilin hakan.
Ɗaga wa na yi iname yin sallama , gaisawa muka yi sannan yake tambaya ta dalilin kashe waya.
Sanar dashi yau muna garinmu na yi sannan na ce "dan Allah ya bawa Hajiya Inna haƙuri gobe insha Allahu damun shigo gari zanzo inda take.
A haka mukayi sallama dashi cike da kewar juna.
In taƙaice maku labari daren yau gaba ɗayanmu ba wanda ya runtsa daga cikin mu farin ciki ya hanamu runtsawa.
Kiran farin muka miƙe muka fara shirin tafiya.
7am Malam ya samo mana shatar mota muka ɗunguma gaba ɗayanmu sai cikin ƙwaryar birnin Sokoto.
Ganin an ɗauki hanyar unguwar su Hajiya Inna na cika da mamaki sai can nace "meyuwa unguwarsu ɗaya ne da Babanmu.
Koda muka isa gidan kaina nada waya ta ina duba mssg ɗin da Ya haidar ya turomin, jin tsayawar mota ne ya sanya ni ɗago kaina , ganin gidan da muke ciki ne ya sanya ni cika da ɗunbin mamaki, sai dai naja bakina na yi shuru iname fatan Allah yasa tunani na ya zamto gaske.
Fitowa mu kayi dukanmu cikin motar kana me mota yaja motarsa ya fice.
Gurinda mutane ke zaune a cikin gidan cikin runfa Baba da Malam suka nufa, inanan tsaye ina kallon ikon Allah sai kawai naga Ya haidar ya miƙe da saurinsa daga cikin mutane ya rirriƙe Babana bakinnan nasa sai wangale sa yake yi.
Ban gama mamakin ba naga dukkanin mutanen gurin sun miƙe suna masu farin ciki suka baibaye Babana.
Gefe muka koma muka yi tsaye muna kallon ikon Allah barma ni.
Ba su ɗauki tsawon lokaci ba muka ga sun yi sashen Hajiya Inna muma haka muka bisu mamaki fall cikin raina.
Da shigarsu Hajiya Inna dake zaune a cikin parlourn tunanin ɗanta fall ranta, sallamar ce ta sanya ta ta ɗago kanta ta kai dubanta ga bakin ƙofar, miƙewa ta yi da sauri ta nufi gurinsu shi ma Baba da saurinsa ya fitar da hannu Ya Haidar daga cikin nasa ya nufi gurinta a sukunye nan da nan ɗakin ya ɗauki rurin kukan Hajiya Inna dana Babanmu, suna riƙe da hannun junansu suka zube a saman carpet suna masu ci gaba da kuka.
Malam ne ya yi gyaran murya sannan ya ce "godiya ya kamata ku yi a gurin Allah ba kuka ba".
Sharewa Hajiya Inna hawaye Baba ya yi itama ta sanya hannunta ta dinga share masa hawayen fuskan sa.
"Gadanga dama kana nan?, ashe kuwa da gaskiyar Shalele daya ce su ne suka ɓatar da kai?, yau gaskiya ta yi halinta, gadanga ina ka shiga tsawon wadannan shekarun?".
Kallonta ya yi cike da soyayyar uwa da ɗa sannan ya ce "alkheree ne ya fitar dani gidannan Hajiya Inna, domin kuwa ina mai farin cikin sanar dake na yi aure harda yara huɗu shekarun da na yi bananan.
Ya faɗa yana me nuno mu da hannu, jiyowa ta yi gurinda ya nuno ai kuwa sai kawai mu ka yi ido huɗu da Hajiya Inna, shi ma Shalelenta ya jiyo yaga ƴaƴan Baban nasa idanuwansa suka faɗa cikin nawa.
A tare su kace "Hadeejatu" nima na ce "Hajiya Inna Ya haidar".
Nan hwa murna ta dawo sabuwa domin kuwa yanzu na sheda Hajiya Inna ita ce mahaifiyar mahaifinmu.
Mu dukanmu mu kaje muka shige jikin Kakarmu cike da so da ƙauna.
Anan Parlourn Hajiya Inna muka zube kana Malam ya ba su labarin tun daga lokacin da suka tsinci Baba har izuwa yau, sosai Hajiya Inna ta yi farin ciki haɗi da yiwa Malam godiya sosai da sosai, shi ma Ya Haidar ya yi matukar farin cikin faɗawan Baba hannu nagari, sosai ya yi wa Malam godiya.
Dakatar da su ya yi da faɗan"ai yi wa kai ne".
Murmushi na yi lokacin daya ce haka.
Anan take Hajiya Inna dani muka cika gabansu Baba da Mama da Malam ga ƴan ƙannena da kayan ciye ciye.
Uban gayyar sai faman shigewa Baba yake yi yana me hamdala da Allah ya nuna masa yau *BABBAN BURI* daya jima dashi a rayuwarsa na ganin ya nemo duk inda ƙanen mahaifin nasa yake sai gashi Allah cikin ikon sa ya bayyana masu shi ba tare da wahalar komai ba......
ƳAR MUTAN BUBARE CE