Atiku, Saraki Da Tambuwal Suna Ƙoƙarin Ganin PDP Ta Miƙa Shugaban Jam'iya A Kudu

Atiku, Saraki Da Tambuwal Suna Ƙoƙarin Ganin PDP Ta Miƙa Shugaban Jam'iya A Kudu


Atiku, Saraki Da Tambuwal Suna Ƙoƙarin Ganin PDP Ta Miƙa Shugaban Jam'iya A Kudu

A binciken da jaridar The Nation ta yi tirka-tirka kan yankin da zai kawo shugabannin jam'iya saboda zaɓen 2023 ya zazafa.

Ta samo bayani 'yan takarar Shugaban ƙasa daga Arewa da haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban majaƙisar dattawa Sanata Bukola Saraki da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamiɗo suna ƙoƙarin riƙe tsarin jam'iyar na 2017  wanda ya sanya Kudu ta riƙe shugaban jam'iya na ƙasa.

Ana hasashen za su iya samun nasara hakan ya sa Kudu maso Arewa sun fara neman shugabancin in da wani gwamna ya nuna sha'awarsa ta tsayawa takara.

Zaman da kwamitin rarraba muƙaman jam'iyar ƙaƙashin shugabancin Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, in Enugu ya kasa cimma matsaya a ranar Alhamis data gabata.

Wasu shugabanni a Arewa sun aminta da tsarin da aka yi a 2017 a cigaba da shi, wannan ƙidirin nasu ya ci karo da buƙatar wasu gwamnoni a yankin Kudu ciki har da Gwamna. Rivers Nyesome Wike.