"Ku Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Kare Ƙuri'un Ku" Sakon  PDP  Ga Mambobinta a Sokoto

"Ku Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Kare Ƙuri'un Ku" Sakon  PDP  Ga Mambobinta a Sokoto

 

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Sokoto ta yi kira ga mambobin ta kan su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kare ƙuri'unsu a lokacin zaɓen gwamnan jihar. 

Jam'iyyar ta yi wannan kiran ne a yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da ta kira  a ranar Alhamis. 
Jam'iyyar ta gudanar da taro ne domin samu hanyoyin da za ta lashe zaɓukan da basu kammala ba na 'yan majalisun tarayya da dattijai  a jihar. 
Da yake jawabi ga mambobin jam'iyar, Bello Aliyu  Goronyo, shugaban jam'iyyar na jiha, ya ce ba su da wani ƙwarin guiwa akan jami'an tsaro kan haka sun ja layi. 
“Ina son da ku fito ku kaɗa ƙuri'un ku a lokacin zaɓe sannan kun yi zaɓe ku tsaya ku kare kuri'un ku." 
"Ku yi duk abinda za ku iya yi domin kare ƙuri'un ku, mu ja layi, Idan wani ya zage ku, ku rama. Idan wani ya buge ku, ku rama kuma." A cewarsa 
Sai dai, a na shi jawabin, gwamna Aminu Waziri Tambuwal, ya buƙaci mambobin jam'iyyar da su daure  duk wani shedani da ya zo rumfa  wanda ya nemi ya kawo hargitsi a lokacin zaɓen. 
“Ina goyon bayan yin abin da addini ya ce, ina son da ku fito ku kaɗa ƙuri'un ku. 
Bayan kun yi zaɓe, ku tsaya ku tsare ƙuri'un ku, ku tabbatar kun tsare har zuwa wajen tattara sakamakon zaɓe." 
“Idan wani yazo tayar da hargitsi, ku kama shi ku ɗaure har sai an kammala zaɓe," a cewarsa.