Babu wanda ya isa ya hana mu yin babban taron PDP - Gwamna Bala Mohammed
Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya, ya ce babu gudu-ba-ja-baya, sai sun gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa a watan Nuwambar shekarar 2025.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya bayyana haka ne bayan kammala taron da suka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Augustan 2025, a jihar Zamfara Inda ya ce sun amince da ci gaba da shirye-shirye, don gudanar da taron a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwambar 2025 a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Gwamnan , ya shaida wa BBC cewa tuni suka sanar da hukumar zabe ta INEC, cewa taron yana nan babu wani sauyi.
Ya ce," Ko a taronmu na koli mun tattauna akan yadda taron namu na kasa zai kasance saboda muna ganin cewa akwai wasu bata gari da ke son kawo mana cikas a cikin jam'iyya ganin cewa jam'iyyarmu ta PDP ta dauko hanyar gyara inda ta zamo abin sha'awa sannan kuma ta zamo jam'iyyar da kowa ke son tsayawa Takara a yanzu."
Bala Muhammed, ya ce," A halin da jam'iyyarmu ke ciki a yanzu babu wanda ya isa y ace ba za a yi babban taro ba, ko ni da nake shugaban gwamnonin PDP, ban isa n ace ba za a yi taro don ba a gaya mini ba, ballantana wani kuma."
"Babu wanda ya fi jam'iyya, domin ita ce ta ce za a yi wannan taro don haka ban ga wanda zai hana ba tun da duk wani tsari da za a bi a ga cewa an yi wannan taro an bi, domin an fadawa Hukumar zabe ta INEC, ta sani kuma zamu je babban taron ne tare da yardarm INEC din."In ji Bala Muhammed.
Gwamnan na Bauchi ya ce," A don haka idan mutum Daya dama yana neman ya kawo akasi, to ba zamu yar da ba domin babu wani mutum nan gaba da zai daga mana kara mu bamu karya ba, haka kuma babu wani da za ice mana kule bamu ce masa cas ba kowayeshi a jam'iyya.
managarciya