Tambuwal Bai Bar Komai a Baitil Malin Gwamnatin Sakkwato Ba---Ahmad Aliyu

Tambuwal Bai Bar Komai a Baitil Malin Gwamnatin Sakkwato Ba---Ahmad Aliyu

 

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya ce ya gadi baitul mali babu ko sisi kuma ko takardar Naira daya tsohon gwamna, Aminu Tambuwal, bai mika masa ba. 

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya amsa tambayar mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayya, Benjamin Kanu, ranar Alhamis. 
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yayin zaiyarar ta'aziyya da ya je, Kanu ya tambayi gwamnan taya ya iya aiwatar da ayyuka 100 cikin kwanaki 100 da hawa mulki. 
Aliyu wanda ya yi magana ta bakin mataimakinsa, Idris Gobir, ya ce sadaukarwa ce kawai domin babu ko kwandala a baitul mali sa'ilin da ya karbi ragamar mulki. 
“Mun gadi Baitul-mali babu ko kwandala, ba abin da za mu iya nunawa, babu takarda ko daya da aka mika mana." 
"Mun sadaukar da kanmu domin sauya akalar jihar nan kuma mun samu nasarar kawo canji a kwanaki 100 na farko." 
Aliyu, ya mika godiya ga jagororin majalisa bisa turo tawaga domin jajantawa gwamnati da al’ummar jihar kan rasuwar abokin aikinsu kuma mamba mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni, Jelani Danbuga.