Mahara Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace Malamin Makaranta A Kaduna

Daya daga cikin al'majiran malamin da aka sace mai suna Idris Abdulrazak, ya ce muna zaune gaban malam muna karatu sai ga wasu mutane dauka da bindigogi suna harbe-harbe suka shigo suka ce mu kwankwanta sai suka fito da malamimmu suka tasa shi gaba suka tafi da shi

Mahara Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace Malamin Makaranta A Kaduna
Mahara Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace Malamin Makaranta A Kaduna

Mahara Sun Kashe Mutum Biyu Sun Sace Malamin Makaranta A Kaduna

A daran juma'a da misalin karfe tara da rabi na dare wasu gungun 'yan bindiga dauke da mugan makamai suka kai hari anguwar Kuregu da ke Wusasa Zariya suka kashe mutane biyu kuma suka tafi da mutane da ba a san yawansu ba ciki har da wani malamin tsangaya mai suna Malam Ibrahim Yakubu Umar mai shekaru 60 da haihuwa.

Tsawon lokaci da yankin Wusasa da ke Zariya ya dauka ba a kai musu hari ba sai ga shi a daran jiya wasu gungun 'yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu, wanda har yanzu ba a san inda matasan suka fito ba, kuma sun tafi da wasu wanda suma ba a san yawansu ba sai dai wani malami tsangaya mai karantar da al'majirai mazaunin anguwar Kuregu a gundumar Wusasa Zariya jihar Kaduna.

Daya daga cikin al'majiran malamin da aka sace mai suna Idris Abdulrazak, ya ce muna zaune gaban malam muna karatu sai ga wasu mutane dauka da bindigogi suna harbe-harbe suka shigo suka ce mu kwankwanta sai suka fito da malamimmu suka tasa shi gaba suka tafi da shi, sai kuma suka kama wasu yara biyu da ke kan Babur roba-roba suka hada su suka yi gaba da su kaji abinda ya faru.

Haka wanda 'yan bindiga suka je gidan sa wanda ya nemi a sakaya sunansa,"ya ce suna shirin kwanviya ke nan sai kawai yaji ana harbi da bindiga sai ya kira 'yan banga tunda dama suna da lamboninsu sai suka ce basu bane toh sai ya gane cewa mugayan baki ne nan da nan sai na kira 'yan tsawon anguwar tare da Jami'an tsaro kafin su zo har sun kashe yara biyu da suka dauko su a kofar gidana.

Da yake karin bayani Sarkin Wusasa Isyaku Danlami Yusufu, ya ce 'yan bindiga sun shigo ne da misalin karfe Tara da rabi amma sun sami dauki daga Jami'an Tsaro cikin gaggawa sai dai 'yan bindigar sun harbe yara biyu da muke zataun suyi ma 'yan bindigar gardama ne inda daya ya muto nan take daya kuma a kan hanyar zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika kuma yanzu haka gawansu na can dan ba a kai ga gane inda suka fito ba, kuma sun tafi da Malam Yakubu Ibrahim Umar malamin tsangaya, kuma a kwai babura guda biyu muna  zataun na wadanda suka kashe ne.