Rikici Ya Bullo: Kotu Ta Dakatar da Ayu Daga Matsayin Shugaban PDP Na Kasa 

Rikici Ya Bullo: Kotu Ta Dakatar da Ayu Daga Matsayin Shugaban PDP Na Kasa 

Wata babbar Kotu mai zama a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ta dakatar da Dakta Iyorchia Ayu daga ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyar PDP na ƙasa. 

Channels tv ta rahoto cewa Kotun ta yi wannan hanin ne har sai ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar dake gabanta, ta ɗage zamam sauraron karar zuwa 17 ga watan Afrilu, 2023. 
Wani mamban PDP daga jihar Benuwai, Terhide Utaan, wanda ya shigar da kara gaban mai shari'a W. I Kpochi, shi ne ya samu umarnin Kotu na haramtawa Ayu nuna kansa a matsayin shugaban PDP.
 A makon da ya shige ne aka dakatar da Ayu kan zargin cin dunduniyar jam'iyya a lokacin da babbar jam'iyyar ke jimamin shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa. 
 Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban PDP, Simon Imobo-Tswam, ya fitar ranar Litinin 27 ga watan Maris, ya ce shugabanni a matakin gunduma ba su da ikon dakatar da Ayu. 
Babban abokin adawar Mista Ayu a cikin jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce ya yi farin ciki da shugabannin gunduma suka kaɗa kuri'ar rashin amincewa da shi.