ZUBAU:Labarin Wasu Makaryata Guda Uku

ZUBAU:Labarin Wasu Makaryata Guda Uku
Daga Rukayya Ibrahim Lawal.
 
 
"Gwaggwo wai da gaske dabbobi suna magana?"
"Kai Arɗo! In ji wane maƙaryacin?"
 
"Gwaggwo wani abokinmu ne yake ba mu labari wai wata rana ya je kiwo shi ne hakan ta...."
 
Baffa ya katse mi shi hanzari da cewa 
"To ko ni nan kwarankwatsa dubu na taɓa jin maganar dabbobi."
 
"Kai Baffa ka ji tsoron Allah yaushe?"
 
"Bantan uban can! Zan miki ƙarya ne Julde? To wata rana ne na raka wani abokina mafarauci jeji. Har ya ɗauki saiti da wata tsuntsuwa zai harba, sai tsuntsuwar ta fashe da kuka ta ce ka min rai Malam mai farauta ina jego ne, jiya na ƙyanƙyashe ƙwayaye goma, ka ga za su zama marayu idan ka harbe ni..."
 
Arɗo ya fashe da dariya.
 
"Gaskiya Baffa ko Zubairu Sarkin maƙaryata ya sara maka."
 
Baffa ya harare shi tare da yi mi shi daƙuwa.
 
Bayan ya zage shi ya ce "Arɗo, yanzu dai faɗa min mi Zubairun ya ce?"
 
"Wai fa Baffa cewa ya yi wata rana ne Inna Jume ta aike shi kiwo sai ya fita tare da karensa Duna. To dama kafin ya bar gida ta ja masa kunne cewa kada ya zalunci dabbobinta. Ya ce to, bayan sun je kiwon sai ya saka sanda yana ta jifgar su. Kawai sai Saniya ɗaya ta hasala ta ce zaluncin ya isa haka Zubairu. Wai sai ya zuba a guje Duna yana biye da shi. Da ya gaji da gudu sai ya zauna yana hutawa ya ce tun da nake ban taɓa jin saniya na magana ba. Buɗar bakin kare Duna sai cewa ya yi nima wallahi ban taɓa ji ba. Ka ji fa wacce ya tsuga mana."
 
Ya ƙarashe zancen yana fashewa da dariya.
 
"Eh wannan kam sai a sara masa, gara nima da gaske ne ya faru, sai dai abin ya so yin kama da almara. Amma wannan labarin na Zubairu kam tantagaryar ƙarya ce."
 
Gwaggwo tana kwashe kwanukan abincin da suka gama ci.
 
"Yo Baffa Ka ga laifinsu? Ai barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba. Gadon ƙarya suka yi fa."
 
Ta wuce tana dariyar ɗa da ubansa.
 
Can kuma ta dawo ta zauna ta kama haɓa.
 
"Wannan gardamar taku ta tuna min labarin da ƙanina Anaruwa ya ba ni...."
 
Arɗo bai jira ba ya ce "Gwaggwo sako taki."
 
"Cewa ya yi watarana yana zaune a tashar jirgin ƙasa kawai sai ga wani jirgi ya zo wucewa, ai kuwa jirgin ya maƙale ya ƙi gaba ya ƙi baya, ana ta al'ajabin hakan. Ko da ya leƙa ƙarƙashin jirgin sai ya ga ashe jinjirin sauro ne ya riƙe tayar jirgin ta gaba, shi ya sa ya kasa motsawa."
 
Ko da Baffa ya ji wannan sai tari ya sarƙafe shi, da sauri ya ja hannun Arɗo.
 
"Cabdijam! Ga uwar Zubairu. Arɗo mu je ka da sauraren wannan ƙaryar ya sanya mu zama makamashin jahannama."
 
Nan fa gwaggwo ta hau ƙyalƙyalar dariya tana faɗar "Na ku wasa ne, ƙaryar ma zubi-zubi ce. Nima dai yau na ɗana."
 
Ƙarshe.
 
Hannunka mai sanda
 
Labari ne da aka kirkira domin bayar da raha ga makarantarmu, da jawo hankalinsu kan su daina daukar karya ba komai ba ce, in suka yi haka za su iya rushe gidajensu ta hanyar yara da matan gida su dauka ai yin karya  wani abu ne na burgewa kamar yadda ka karanta a rubutun nan.
Kiranmu ga jama'a a guji karya a cikin kowane lamari don samun tsira da tarbiya mai inganci.