LISSAFIN KADDARA: Fita Ta 3 & 4

LISSAFIN KADDARA:
*Ibnatu Sulayman*
*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*
P*3&4
Gaba daya Umma ta rude ta gigece a cikin wanda suka kawo Khadija kuwa kowa yayi shiru suna kallon ta sai da makota suka shigo suka kama Khadija aka shiga daki da ita,ita kuma Ameenatuh aka yayyafa mata ruwan sanyi bayan ta farfado gaba daya akayi daki kan Khadija da take fitar da numfashi da kyar gaba daya jikin Ameenatuh karkarwa yake batason rasa 'yar uwar ta a wannan halin da suke ciki gashi likita ya tabbatar mata 'yar uwarta tana cikin matsanancin hali dake barazana ga rayuwarta gashi sun nemi taimako har yanzu shiru ba mai niyyar taimaka musu,haka suka sa Khadija gaba sai dai kuka kawai,ganin kukan bazai kaisu ba yasa ta tashi tashiga makotansu neman aron kudin motar da zai kaisu asibiti sai dai har ta gama yawonta bata samo ko biyarba haka ta dawo suka zubawa sarautar Allah dan kukanma ya daina zuwa yunwa kuwa bama maganarta akeba dan sai kana da kwanciyar hankali kake gane kana jin yunwa ko akasin hakan, sallamar Alhaji Sama'ila ce ta katsewa kowa tunanin da yake Ameenatuh kam tama kasa tashi bare kuma akai ga batun Umma da gaba daya jikinta ya saki batama iya wani motsin kirki"wai ko ba mutane a gidan ne!?"yayi tambayar cike da kufula "ka shigo" Ameenatuh ta amsa a sanyaye ba shiri ta kara fusatashi "da shigowa nake in nazo kajimun munafukar yarinya"ba shiri ta dafa bango ta mike kai tsaye soro ta nufu tana dafa bango zuciyarta na tsananta bugawa "yi hakuri Baba Sama'ila Khadija ce ba laf...."saurin katseta yayi ta hanyar daga mata hanannu "ya isa Malama a gidan uban wa na zama babanki da zaki cemun baba in kunaso ku cuci mutum sai ku kama kwantar dakai da karya harshe to wallahi ba'a nan ba,Dan yau zaku bar min gida mayun banza mayun wofi shekara uku kenan duk shekara sai dai a unguwa ayi muku karo-karo to wallahi wannan karon ko an hada muku sai kun barmin gidana tunda ban hada da gadon ubanku ba! kullum sai an tabaku kuce ba lafiya saboda ku kuka kawo cuta duniya" ya karasa maganar yana huci hade da hura hanci da zare ido,kanta na kasa har ya gama masifarsa sannan ta dago idonta cike da hawaye tace"shikenan Baba Sama'ila amma Dan Allah kayi mana alfarma ta karshe ka barmu zuwa jibi in Sha Allah zamu tashi tunkan kazo"kallon da yayi matane yasa ta zube bisa guiwowinta ta hade hannunta guri guda tace"dan sonka da manzon Allah s.a.w kayi mana alfarma zuwa jibin dan Allah" wanda zukazo tare ne yace "shikenan yarinya kije ku shirya zuwa jibi yawar haka kar mu sameku a cikin gidan nan"godiya tayi sosai suka wuce ita kuma tashiga ciki a tsakar gida ta samu guri tayi dabar shekarunta basukai su na dauka kalar damuwar da take dauka ba shekarunta 15 gaba daya wanda baici ace muguwar damuwa tana huda zuciyarta haka ba, bahaushe yace"ba'a sabo da wahala"da anayi da Ameenatuh sun dade da sabawa da ita,mikewa tayi ta shige dakin tana sakawa da warwarewa ta zauna a gaban khadija da bacci yayi gaba da ita sai dai kana kallonta kasan ba baccin dadi takeyi ba sai da ta tabbatar khadija tayi nisa a baccinta sannan ta guyo ta fuskanci Umma kafin tace"Umma in Sha Allah anjima zanje aikin daren kodan na samu nakai khadija asibiti gobe kuma kinga in Allah ya taimakemu mu samu a siya mana magani amma dai zaman bazai yiwu ba ba madafa ba Umma ya kamata mu nemi mafita tun kafin mu fara bushewa da ranmu, kuma Alhaji Sama'ila yace zuwa jibi war haka mu tashi,
A jiyar zuciya Umma ta sauke sannan ta danyi murmushi wanda hausawa sukace"yake yafi kuka ciwo" kallon Ameenatuh kawai take tana girgiza kai kafin a hankali ta furta "duk ni ce sanadi,duk ni najefaku a cikin wannan rayuwar mara madafa Ameenatuh dan Allah ku yafemin ke da 'yar uwarki"ta karasa maganar kuka na sarketa,matsawa Ameenatuh tayi ta rungumi Umma da kyau sannan tace"haba Umma kema kinsa kowa da kalar tashi kaddarar mu wannan itace ta mu bama zargin kece sanadi Umma Abbanmu shine sanadin komai kuma dama can Allah ya riga ya rubuta mana tamu kaddarar a haka wata kila in mukayi aiki mai kyau wajen cinye jarabawarmu batare da sarewa ko nuna damuwa ba Allah ya canza mana ita ta koma kyakkyawa"kuka suke sosai sun kankame juna an rasa wa zai bawa wani baki yayi shiru haka suka gaji sukayi shiru jin kiraye-kirayen sallah yasa suka tashi suka gabatar da ita akan lokaci,
6:40pm ta fito cikin shirinta na zuwa wajen aiki Umma ta samu a tsakar gida sai khadija dake kwance cinyar Umman idonta rube ka kallonta kasan idonta biyu shiru kawai tayi "Umma ni zan wuce sai da safe in Allah ya kaimu,ke kuma Khadija ki kiyayeni wallahi banason yawan tunanin nan da kike nama rasa tunanin mai kike ko yunwa kike ji?" kai kawai Khadija ta daga alamun eh "to shikenan ina da hamsi in siyo miki garin kwaki zaki sha haka ko na siyo miki biscuit?""ki siyon garin zai danfi rike ni" kallon Umma Ameenatuh tayi tana murmushi sannan tace"Umma bari naje zan aiko mata garin daga can zan wuce kimun addu'a a sallahrki yau, Khadija sai na dawo"tana gama fada tayi addu'ar fita daga gida ta fice,a hanya ta sai garin ta bawa dan mako tansu ya kaiwa Khadija,da sallama yashi sai da ya gaida Umma sannan ya bata sakon ya fice,garin kwaki ne rabin kwankwani dan yanzu gari kwankwani naira dari ne ,cikin azama Umma ta tashi ta cikawa Khadija garin ita kuma taja gefe ta zuba uban tagumi "Umma mu sha mana ai naga kema bakici komai ba"murmushi Umma tayi kafin tace"ai nasha ni ma dazu lokacin kina bacci ki sha kawai",
6:58mp ta isa company da suke aikin qaron sai dai tasha mamkin yadda har 12:00am bataga Oga ba sannan a cikin manyan gurin ba wanda ya tambayi ya lafiyar Khadija,abun ba karamin dadi da daci yayi mata ba abunda yayi mata dadi rashin ganin ogan su saboda dama ita shine barazana a gareta da rana ma bare kuma dare ya tsala,abunda kuma yabata haushi shine rashin tambayar jikin Khadija da manyan gurin ba suyi ba tashi tayi daga tsintar karon da take ta koma gefe jikin fanfo ta dauro alwala ta zo ta shimfida dankwalinta ta gabatar da nafila raka'a biyu ba tare da ta tsawaita ba tana idarwa ta dora da addu'a wanda duk abunda taroka akan Khadija ne,
Da sanyi safiya ta koma gida cike da farin ciki dan kuwa tayi aiki a daren nan mai kyau buhu hudu tayi na karo hakan yasa ta tashi da naira dubu hudu abunta tunkan ta karasa gida ta tsaya ta siya musu shinkafa kwata wanda kudinta ya kama naira 1000 ta siya musu man gyada da kayan da duk ake bukata kama daga ice kayan yaji a haka dai ta kaso 1800 a hanya taga mai awara ta siyawa Khadija ta 200,
kudi maisa nishadi yanayin yadda ta shiga gidan shi kadai ta fahimtar da Umma yau Ameenatuh tayi samuwa sunan zaune a tsakar gida kamar jiya Khadija na kwance jikin Umma jin sallamar Ameenatuh ne yasata tashi kamar mai tausayin kasa haka take motsa jikinta sai Umma ce ta karasa daga ta itama dai da kyar take motsi,kayan hannun ta ta aje ta karasa gun Umma ta gaida ita sai da suka Gama gaisawa sannan Khadija itama ta gaisheta cike da girmamawa tare da yunkurin komawa ta kwanta Ameenatuh ta dakatar da ita ta hanyar taro keyarta tana murmushin yake dan ita kanta motsin da kyar takeyinsa rabonsu da suci abinci yau kwana uku kenan sai jiya da suka samu suka kurbi kunun sadaka,
Awarar ta janyo cikin ledodin da ta shigo da su tana cewa "Umma yau 'yarki tayi abun kirki na fada miki yau buhu hudu nayi na karo gashi naje makotan company mu da ake aikin citta sun dauke ni aikin rana"kallon ta kawai Umma take har ta gama magana sannan ta magantu da"Allah ya miki albarka Ameenatuh Allah ya baki miji na gari wanda zai kula da ke fiye da yadda kikeyi da mahaifiyarki nagode Ameenatuh nikam ba abunda zancewa Allah sai godiya saboda ya baniku amatsayin garkuwa""ameen Umma muma mungode bisa tarbiyyarki garemu, Khadija ga awara na siyo miki nasan bakya jin dadi da kyar in zaki iyacin shinkafa,ya jikin naki ma wai"lumshe ido Khadija tayi tana jayo ledar gabanta "nagode sister Allah ya saka da alkairi,sun baki kudin aikina na jiya kuwa""kyalesu suna raina hakki ne kuma hakki duk hakki ne duk kankantarsa, bari mugama girki muje asibiti"awarar ta dauka tana kaiwa bakinta tare ta furta kalmar Bismillah tace "Umma dauki awarar sister kema dauki kan a gama abinci" ba musu suka dau dai'-d'ai kowa yasa abakin salati...