An Ɗauke Wutar Lantarki A Faɗin Najeriya Kan Matsalar Da Ta Samu

An Ɗauke Wutar Lantarki A Faɗin Najeriya Kan Matsalar Da Ta Samu

Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya a safiyar Alhamis.

Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) ta cika shekara guda ba tare ɗaukewar wutar gaba ɗaya ba kamar yadda aka saba a ƙasar.

Wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu (EEDC) ya fitar a safiyar ta ce wutar ta fara ɗaukewa ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare ne.

Sakamakon haka, “duk tashoshinmu ba su da wutar lantarki da za su raba a jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo.”

Aminiya ta gano cewa ƙarfin wutar lantarkin kasar ya ragu zuwa megawatt 273 daga cikin biyu daga cikin cibiyoyinta 27.