Gidauniyar Dan Majalisar Tarayya Ta Bayar Da Tallafi Ga Masu Lalura Ta Musamman A Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Gidauniyar dan Majalisar tarayyar Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin zuru, fakai, Danko wasagu, da Sakaba da ke jihar kebbi, ta kaddamar da rabawa marassa Galihu kekunan Guragu domin saukaka musu al'amuran yau da Kullum.
An tallafawa marassa Karfi Guragu kekuna domin cigaban rayuwar su, duba da yadda suke tafiya acikin mawuyacin hali.
Gidauniyar tallafawa marassa Karfi da nakasassu ta dan Majalisar, ta ba da tallafin kekunan Guragu ga masu bukata da suka fito, daga kananan hukumomi guda hudu, a fadin jihar kebbi.
Tunda farko dai Shugaban gidauniyar da yake gabatar da jawabinsa a yayin gudanar da taron Malam Bala Manga, ya bayyana cewa dan Majalisar ya nemo wannan tallafi ne, duba da halinda nakasassu suke ciki na rashin kyautatuwar rayuwa.
Bala Manga, bayyana farin cikin sa sosai a kan yadda Tukura ya himmatu matuka domin ganin marassa Karfi sun samu walwala kamar yadda kowa yake samu a kowane mataki na rayuwa.
karshe Shugaban Guragu ya yi jawabin godiya amadadin sauran guragu da nakasassu na wannan yankin ya kuma ya bama dan Majalisar akan kokarinsa da yake na kula da al'ummar mazabarsa.
managarciya