An Bayyana Muhimmancin  Zakka Da Waqfi Wajen Yaƙi Da Talauci A Ƙasashen Musulmi

A takardar bayan taro da aka fitar, ƙungiyoyin da haɗin gwiwar Jami'ar Al-Istqamah sun bukaci gwamnatoci a dukkan natakai, musamman jihohin da ke da rinjayen Musulmi su samar da ingantattun dokoki da tsarin yadda za a riƙa tattarawa da amfani da Zakka da Waqafi yadda ya dace.   Har wa yau sun kuma koka da yadda har yanzu mawadata da masu hannu da shuni suke nuna halin ko in kula wajen fitar da Zakka, ta yadda za ta amfanar da al'umma bisa koyarwar addinin Musulunci.   An ba da kyakkyawan misali da yadda Gwamnatin Jihar Sakkwato ke tafiyar da harkokin hukumar da ke kula da tattara Zakka da Waqafi ta jihar wanda ya nuna lallai tsarin koyarwar addini game da tallafawa raunana zai iya aiki a ko'ina, kuma ya amfanar da al'umma da dama.

An Bayyana Muhimmancin  Zakka Da Waqfi Wajen Yaƙi Da Talauci A Ƙasashen Musulmi

 

Gamayyar haɗin gwiwar ƙungiyoyin ma'aikatan hukumomin kula da tattara Zakka da Waqafi ta Nijeriya (AZAWON) da Jami'ar Musulunci ta Al-Istqamah da ke Sumaila a Jihar Kano sun gudanar da wani taron haɗin gwiwa, da nufin ƙara wayar da kan juna muhimmancin tattara Zakka da Waqafi a koyarwa addinin Musulunci, da kuma samar da shawarwari na yadda za a yi amfani da dukiyar da ake tarawa wajen sauƙaƙa rayuwar al'umma marasa ƙarfi da mabuƙata.

 

Taron wanda aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Zakka da Waqafi ta Jihar Sakkwato, Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki, ya mayar da hankali ne wajen tattauna rawar da Zakka da Waqafi za su iya takawa wajen rage raɗaɗin talauci a tsakanin talakawan ƙasar nan da ma sauran ƙasashen Musulmi.

 
A takardar bayan taro da aka fitar, ƙungiyoyin da haɗin gwiwar Jami'ar Al-Istqamah sun bukaci gwamnatoci a dukkan natakai, musamman jihohin da ke da rinjayen Musulmi su samar da ingantattun dokoki da tsarin yadda za a riƙa tattarawa da amfani da Zakka da Waqafi yadda ya dace.
 
Har wa yau sun kuma koka da yadda har yanzu mawadata da masu hannu da shuni suke nuna halin ko in kula wajen fitar da Zakka, ta yadda za ta amfanar da al'umma bisa koyarwar addinin Musulunci.
 

An ba da kyakkyawan misali da yadda Gwamnatin Jihar Sakkwato ke tafiyar da harkokin hukumar da ke kula da tattara Zakka da Waqafi ta jihar wanda ya nuna lallai tsarin koyarwar addini game da tallafawa raunana zai iya aiki a ko'ina, kuma ya amfanar da al'umma da dama.
 
A yayin da aka shawarci malamai da ma'aikatan da ke aikin tattara Zakka da Waqafi su ƙara zafafawa wajen wayar da kan jama’a muhimmancin fitar da haƙƙin Allah a dukiyoyin su, a minbarorin wa'azi da kafafen watsa labarai, mahalarta taron sun kuma yabawa mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na lll bisa yadda yake ƙarfafa al'amarin samar da Gidauniyar Zakka da Waqafi, don taimakawa Musulmi a ƙasar nan.
 
Taron ya kuma buƙaci ma'aikatan da ke gudanar da wannan aiki su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukan da suke yi, da kuma tabbatar da suna adana dukkan bayanan da suke shigarwa da fitarwa, don tsare gaskiya da adalci.
 
Daga Mukhtar A.  Halliru Tambuwal, Sakkwato