Buhari Ya Sanya Hannu Kan Dokar Zabe, Ya Kuma Sanarda Majalisa Abin Da Yake Son Ta Yi  

Buhari Ya Sanya Hannu Kan Dokar Zabe, Ya Kuma Sanarda Majalisa Abin Da Yake Son Ta Yi   

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar zabe da majaisar tarayya ta yi wa gyaran fuska domin tun karar zaben 2023.

Shugaban kasa ya saka hannun ne a  ranar Juma'a  a fadar gwamantin tarayya dake Abuja in da  Shugaban majalisar dattawa dana majalisar wakilai suka halarta.

Buhari bayan ya saka hannu  kan dokar,  ya bukaci 'yan majalisar da su hanzarta yin gyara ga sashe na 84 na dokar wanda ya tanadi haramta wa masu rike da mukaman gwamnati jefa kuri'a a zaben shugabannin jam'iyya ko kuma na 'yan takara.

 

Shugaban ya ce wannan sabuwar dokar zaɓen, za ta ƙara inganta harkar zaɓe ta hanyar tabbatar da an yi abubuwa a bayyane ba tare da nuƙu-nuƙu ba a lokacin zaɓen da kuma rage abubuwan da za su ja ‘yan takara su yi ta ƙorafe-ƙorafe.

Shugaba Buharin ya bayyana cewa wannan ƙoƙarin na sanya hannu kan dokar zaɓen na daga cikin tsare-tsaren gwamnatinsu na ƙara buɗe hanya domin gudanar da sahihin zaɓe mai inganci.

 

Ya kuma ce babu wani mai riƙe da muƙamin siyasa da zai iya zama wakilin masu zaɓe wato 'dalaget' ko kuma a zaɓe shi a yayin babban taron jam'iyya domin ya tsaya takarar zaɓe.