A Ƙasar Saudiya An Karrama Shugaban Matasan Ƙadiriya Na Jihar Sakkwato   

A Ƙasar Saudiya An Karrama Shugaban Matasan Ƙadiriya Na Jihar Sakkwato   

A Ƙasar Saudiya An Karrama Shugaban Matasan Ƙadiriya Na Jihar Sakkwato   

        

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.

  
Wasu bayin Allah, 'yan uwa da masoya na birnin Madina, kasar Saudi Arebiya, sun shirya walimar  karram Sheikh Ahmad Dikun Dikun akan Sarautar da ya samu ba da jimawa ba ta uban Doman Kilgori, wadda uban kasar Kilgori, Sai'in Kilgori,ya ba shi.    
A lokacin walimar an ci an sha an yi nasihohi, kana an yi addu'a ta musamman domin samun dawowar zaman lafiya a jihar Sokoto da kasa baki daya. 
Sheikh Dikun Dikun wanda ake yi wa lakabi da limamin Vila yayi godiya ga dukkan sauran 'yan uwa da masoyan da suka shirya walimar da wadan da suka samu damar halarta da wadan da suka izo sakonnin su na fatar alheri. Walimar ta samu halartar wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Saudiya   da suka hada da sheikh Abdallah Bukur Al-Hausawey da sheikh Ya'akub Alhajjamen da wasu sarakuna da malamai da dama sun samu halartar taron.