Allah Gwani: Ka San Kuɗin Iskar Da Kake Shaƙa Duk Awa?

Allah Gwani: Ka San Kuɗin Iskar Da Kake Shaƙa Duk Awa?

A yayin da kake numfashi a sauƙaƙe kuma a ɓagas bisa horewar Ubangiji, wani yana can sai ya siya duk awa.

Numfashi musayar iska ne da ke gudana a huhu tsakanin mutum da muhallinsa.

Muna shaƙar iskar oksijin sannan mu fitar da gurɓatacciyar oksijin zuwa muhalli.

Marasa lafiya da ke fama da cutukan huhu ko numfashi da kuma cutukan zuciya suna gaza wadatar da kansu da oksijin har sai an taimaka musu da tukunyar oksijin a asibiti domin yin numfashi.

Sai dai, wannan oksijin siya ake duk awa saɓanin wacce muke shaƙa a muhalli a kyauta.

Wani rahoto da jaridar Daily trust ta wallafa ranar Asabar, 19 ga Yunin 2021, ya nuna cewa a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano (AKTH), da ke Kano, ana biyan ₦800 duk awa ɗaya domin oksijin ga manya, inda ake biyan ₦400 ga yara.

Haka nan, rahoton ya sake nuna cewa a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase (Asibitin Nassarawa), da ke Kano, ana biyan ƙasa da ₦500 ga manya.

Wato idan mara lafiya yana biyan ₦800 kowace awa, idan ya kwana ɗaya tak, wato awa 24, zai biya ₦19,200 na oksijin kawai, banda kuɗin gado, magani, gwaje-gwaje da sauransu.

Hmm! Mai lafiya ɗan-gata.

Allah ya ƙara mana lafiya. Marasa lafiya na gida da asibiti Allah ya ba da lafiya.