Nan Gaba Kadan Kiyon Lafiya Matakin Farko Zai Inganta a Sokoto---Dakta Larai Tambuwal

Nan Gaba Kadan Kiyon Lafiya Matakin Farko Zai Inganta a Sokoto---Dakta Larai Tambuwal

 

 Sakatariyar zartarwa a hukumar kiyon lafiya matakin farko a jihar Sokoto Dakta Larai Aliyu Tambuwal ta fadi yanda take ganin nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar Sakkwato karkashin gwaman Dakta Ahmad Aliyu Sokoto  za ta bunkasa harkar kiyon lafiya matakin farko ganin yadda bangaren ya yi doguwar suma.

Dakta Larai Aliyu ta sanar da kudirin gwamnati ne a lokacin da ta fita zagayen duba yadda aikin bayar da allurar rigakafin cutar shan inna(polio) ke tafiya a karamar hukumar Dange Shuni  in da ta yaba da aikin tare da ba da shawarwari ga ma’aikatan.

Dakta Larai ta sha alwashin nan gaba kadan, kiyon lafiya a matakin farko zai inganta a Sokoto, Gwamnan jiha ya damu da lafiyar al’umma don cimma manufar da aka sanya a gaba akwai bukatar mutane su daina siyasantar da harkar lafiya a cigaba da mutunta juna a cikin aiki hakan zai bunkasa kiyon lafiya.

“Gwamnatin nan a shirye take ta samar da kayan aikin kiyon lafiya ga ma’aikata domin ganin an cimma burin kawar da duk wata cuta dake barazana ga lafiyar mutane a jiha.”

Dakta ta nemi mutane su bayar da hadin kai ga masu bayar da rigakafin Polio, domin wannan wani samfurin cutar ne aka gano yana yaduwa a cikin mutane, da ake son yara su samu rigakafi da zai sa garkuwar jikinsu ta yi karfin da za ta iya kare shigar cutar gare su.

Dakta  Larai ta ce don ganin an bunkasa kiyon lafiya shirin tura ma’aikata a wasu jihohi na wuccin gadi saboda farfado da kwazonsu za a dawo da shi ganin yadda wasu ma’aikata ke wasa da aiki, bayan bukatar da ake da ita a koyaushe ana son ma’aikacin lafiya na samu sabuwar basira.