Babu Sunan Osinbajo a Jerin Kwamitin Kamfen Tinumbu
Har zuwa yanzu ba a ga sunan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a cikin jerin sunayen ‘yan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta fitar ranar Juma’a ba,
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren Apc James Faleke, wadanda aka zaba za su karbi wasikun nasu nadin ne ranar Litinin, in da za a kaddamar da su.
An fitar da jerin sunayen in da aka sanyan gwamnoni masu ci da tsoffi da wasu tsoffin ministoci, yayin da ministocin Buhari ke da karanci a cikin kwamitin.
managarciya