A shekara ɗaya an yi wa yara ƙanana 1,114 fyaɗe a Sakkwato

A shekara ɗaya an yi wa yara ƙanana 1,114 fyaɗe a Sakkwato

 

Masu ruwa da tsaki a jihar Sakkwato sun yi tir da yanda harkar fyade ta yawaita a jihar,  abin damuwa ne kwarai musamman yanda ake haifuwar yara ba ta hanyar aure ba, sun yi kira da a dauki matakin magance matsalar.

Rabi'u Bello Gandi ma'aikaci a kungiyar  save the child inititive, kodinata kungiyar kare da hana cin zarafin dan adama a jihar Sakkwato ya ce "a shekarar 2020 abin ya waita  ya kara karuwa har zuwa 2022, daga nan lamarin ya fara ragewa domin matakin da ake dauka, 2023 karshenta abin ya yi sauki sosai.

"A shekarar data gabata muna da kididdiga wadanda suka kawo koken yi masu fyade a wurin hukukuma adadin yakai 1,114, su ne muke da su a rubuce," a cewarsa.

Kuna da tunanin hada mazan da suka yi fyade da matan da aka yiwa aure don rufe magana? ya ce "mu yadda muke yi ba mu karfafa hakan ba, domin duk wanda ya yi maki fyade baya sonki, mazan ba su bukatar auren wadan da suka yi wa fyade, abu na biyu in kun hada auren wata biyu zuwa uku sai su sake su tun da addini bai hana mutum ya saki matarsa ba, babu hukunci don ya aure ta ya saki, shi ne dalilin da mun fi ba da muhimmancin kulawa ga wanda aka ci zarafinsu da ba shi shawara har ya dawo da hayacinsa ya dauka abu ne da Allah ya kawo bai wuce ya faru da kowa ba, sai mu koya masa sana'a don tsayuwa da kai domin mafiyawanci rashin sana'a ce ke sa suna samun kansu a wannan yanayi, in sun haifi yara za a reno su har su kai ga wani mataki don amfanin al'umma."

Kodineta Rabi'u Gandi ya cigaba da cewa hukumarsu na kokarin wayar da kan al'umma  kuma gwamnati ta yi abin da ya dace kan 'yan gudun hijira a kula da su kar su samu kansu a cikin yanayin da rayuwarsu za ta lalace, ana kawo mana korafi wasu na amfani da halin da suke ciki domin  cin zarafinsu.

Huldarku da malaman addini? ya ce "aikin da muke yi na wayar da kan al'umma tare da malamai muke yi wadan da ke fadakar da mutane laifi ne aikata zina balle ma fyade, da sanar da su dokar da aka kafa a jiha kan cin zarafin mata da kananan yara, duk da iri-iri ne akwai wanda ake yi a tsakanin ma'aurata da 'ya'ya dukan su muna aiki da malamai don samar da maslaha da zai sa asamu al'mma ta gari.

"A shekarun baya mutane ba su fadi in yi masu fyade domin suna ganin ba a komai amma a yau  sukan kawo rahoto gare mu bayan mun fada masu duk wadda aka ci zarafinta za mu kwato mata hakkinta kuma sun ga ana hakan, har yau ana kawo mana rahoto wannan shiri ne na kungiyoyi masu zaman kansu da malaman addini da shugabannin al'umma suka sadaukar da kansu domin ganin an yaki lamarin, ana samun cigaba.

"Talla na cikin ginshikin abin da ke kawo fyade a yanzu talla ba raguwa ta yi ba saboda halin matsi da ake ciki na tattalin arziki, a koyaushe muna wayar da kan jama'a yaro ya rinka yin talla a wurin da ke da mutunci da tsafta a in da ake iya sanya masa ido, sakin yara Almajirai bai dace ba yakamata uwaye su rika kula da yaransu don ya samu zama mai amfani.

"In aka ci gaba da hukunta duk wanda ya aikata fyade gwargwadon yanda doka ta ce, samar da aikin yi ga mutane, uwaye su rika bayar da hadin kai in aka samu fyaden  wadannan za su kawo raguwar aikata fyade a cikin al'umma.