Tambuwal ya fifita siyasa kan rayuwar al'ummar Sakkwato-----Malami Bajare

Honarabul Malami Muhammad Galadanci da aka fi sani da Bajare ne ya sanar da hakan a zantawarsa da Managarciya a Sakkwato ya ce daTambuwal yana kishin jama'ar jihar nan da ya jingine halartar taron siyasa har sai an shawo kan matsalar tsaron da yankin Gabascin Sakkwato ke fuskanta, amma ba ruwansa.

Tambuwal ya fifita siyasa kan rayuwar al'ummar Sakkwato-----Malami Bajare

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya fifita harkokin siyasarsa da jami'iyarsa ta PDP kan rayukka da dukiyoyin jama'ar jihar Sakkwato.

Honarabul Malami Muhammad Galadanci da aka fi sani da Bajare ne ya sanar da hakan a zantawarsa da Managarciya a Sakkwato ya ce daTambuwal yana kishin jama'ar jihar nan da ya jingine halartar taron siyasa har sai an shawo kan matsalar tsaron da yankin Gabascin Sakkwato ke fuskanta, amma ba ruwansa.

"Ka dubi yanda aka kashe jami'an tsaron ƙasar nan sama da 20 amma gwamna bai je in da abin ya faru ba, bai jajantawa iyalan mamatan ba, balle ya kira su a gidan gwamnati ko ya je gidajensu don ya taimaka masu da wani abu da zai rike su, kafin hakkin mazajensu da suka rasa ransu a wurin kare rayuwar jama'arsa ya fito.

"A jawabin da Tambuwal ya fitar na jinjinawa sojoji masu rai ya manta da margaya,  ya yi aiki ne da saƙon da rundunar hadarin daji suka fitar kawai ba tare da ya je ya ganewa idonsa ba matsayinsa na gwamna." a cewar Bajare 
Haka ma ya ce "a lokacin da Tambuwal yake Kaduna kan wane yanki ne zai samar da Shugaban ƙasa, ya kuma zarce Abuja kan taron jam'iyarsu a batun karɓa-karɓa a lokacin ne ake kashe mutanen Gangara da Gatawa a ƙaramar hukumar Sabon Birni, ina kishi anan bai taɓa zuwa wuraren da mutanen Sakkwato ke gudun hijira a Nijar da wasu wurare a Sakkwato."

"Tambuwal ya yi bukin ƙaddamar da rabon babura ga 'yan banga a Sakkwato amma har yanzu ba wani mutum ɗaya da aka baiwa babur balle a ƙarfafa su da tallafin na Mai don gudanar da sintiri a yankunansu.

"Ba ka jin Tambuwal ya je Tangaza ko Gudu ko Sabon Birni ko Isah kan matsalar tsaro amma za ka ji a wasu wurare don gudanar da siyasa, yakamata ya sani shi fa ba ɗan majalisa ba ne Gwamna ne a jihar Sakkwato," a cewar Malami.