2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Za su Gyaru Cikin Sauki---Sanusi Ya Fadawa  'Yan Najeriya

2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Za su Gyaru Cikin Sauki---Sanusi Ya Fadawa  'Yan Najeriya

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya shawarci yan Najeriya da kada su zabi duk dan takarar shugaban kasar da yayi ikirarin cewa abubuwa zasu yi sauki da zarar an zabe shi a 2023. Sanusi wanda ya kasance shugaban darikar Tijanniya na kasa ya bayyana hakan a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, a wajen rufe taron tattalin arziki da zuba hannun jari na Kaduna, The Cable ta rahoto.

“Dan Allah bari na nemi wani abu daga yan siyasarmu. Dole ku shirya zukatan yan Najeriya game da daukar matakai masu wahala. 
“Duk wanda ya fada maku cewa abubuwa zasu yi sauki, dan Allah kada ku zabe shi. Imma dai yana maku karya ko kuma bai san wani irin aiki zai samu bane. 
“Da wannan tarin basussuka, da wannan tarin rugujewa a kudaden shiga, da wannan talauci, ba z aka iya daukar matakan daidai ba. Ya zama dole a gyara haraji kan ma’aikatar lantarki. Ya zama dole a gyara haraji a ma’aikatar mai. 
“Amma kafin a gyara wannan, dole mu magance damammaki na neman rancen kudi. Ya zama dole a dinke barakar da ke lambobin, lambobin karyan.”