AMFANIN TSAMIYA A JIKIN DAN ADAM DA MATSALAR DA TAKE HAIFARWA
1. Tsamiya na Magance Matsalar Cushewar ciki da rashin yin bahaya.
2. Tsamiya na Maganin Mura da zazzabi me Zafi ajikin Dan Adam.
3. Ruwan Tsamiya na Magance Ciwon ciki.
4. Tsotsar Tsamiya na Magance Matsalar Tashin zuciya ga mata masu ciki.
5. Tsamiya na Magance Matsalar Tsutsar ciki.
6. Tsamiya na Magance Matsolin da suka shafi hanta da madaciya.
ILLOLIN TSAMIYA A JIKIN DAN ADAM
1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda ta na rage adadin sikarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi tiyatar saboda wannan dalili.
2. Ramewa. Yawan shan tsamiya na iya kara rama ga Masu Kananan Jiki. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba
3. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibrofen da Aspirin saboda ta na kara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.
_AMH - ISLAMIC HERBAL_
managarciya