WATA UNGUWA:Fita Ta 16
BABI NA SHA SHIDA
DAWOWA DAGA LABARI
Bayan ficewar Baba Mudi daga gidan Inna ta koma kan tabarma ta zauna tana jin zogi a idonta a bayyane ta ce "Wannan wace irin Zuciya ce gare ka Mudi? Ji yanda kake neman makantar da ni, baya ga wannan ɗanyen aikin da ka yi kan ƴaƴana."
Su kuwa su Hanifa sai da suka tabbatar da ya bar gidan kafin su sake juna, kowa ta koma makwancinta sai kuka suke kaɗan-kaɗan.
Ba ma kamar Hanee da take jin wata iriyar azaba tun lokacin da ya shauɗa mata bulala a saitin inda aka mata ɗinki, Allah ma ya kare ɗinkin bai walwale ba ai da bata ma san yanzu a wane hali take ciki ba.
Inna ma tana can tana fama da kanta, bata sake ko leƙo su ba, balle ta ga halin da suke ciki, wannan fa shi ake kira haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance.
Suna nan a hakan Mankas ya shigo gidan ya sha ya yi Mankas, sai layi yake kamar zai kifa.
Bari zancen sallama don har ya manta yanda ake yinta, a haka ya nufi ƙofar ɗakinsu Hanifa cikin Muryar maye yake faɗar "Ina wannan tantiriyar ɓoyen? ki fito ki ban wani abu yau ko na tona asirinki a cikin gidan nan." Yana maganar ne yana ƙara kusantar ɗakin.
Ras! Kirjin Hanee ya buga da ƙarfi a ranta ta ce 'Shike nan na shiga ɗari, ya je ya sha abunsa zai zo ya tonan asiri.' nan take ta nemi zogin ciwon da take ciki ta rasa, da ƙarfi ta yunƙura ta nufi ƙofar, tare da tarbe shi kafin ya ƙaraso ciki.
A dai-dai lokacin inna ke faɗar "Allah ya shirye ka Suleman! Yau ma abun ka shawo ko? Wa kake faɗar zaka tonawa asiri?." Ta yi maganar kamar mai shirin yin kuka.
Har ya buɗi baki zai yi magana Hanee ta yi saurin saka hannunta ta toshe masa baki, da yake Innar tana nesa da su a bayan katangar ɗakin take, saboda haka bata iya hangensu sai dai ta ji sautin.
"Ina jinka Suleman da wa kake magana?." Innar ta kuma faɗa.
A hankali Hanifa ta je saitin kunnansa ta raɗa masa wata maganar, sai ga murmushi ya bayyana a fuskarsa duk kuwa halin da yake ciki.
Daga can ya ɗago muryarsa da har yanzu bata sake ba ya ce "Gaskiya Inna kin cika sa ido, kina yawa fa."
Ai Inna na jin haka, ta wuce ɗakinta cikin hanzari, 'yar kwallar da ta taru a idonta tana neman shanyewa, sai ga shi ta zubo.
Tabbas kuwa dama 'yan magana sun ce 'duk abinda ka shuka shi zaka girba.' yau dai ga shi tana girbar sakamakon fanɗarewa da rashin girmama iyayenta da ta yi a baya.
A ƙasan yagaggiyar ledar ɗakin ta zauna tana tunanin baya.
A take majigin ƙwaƙwalwarta ya shiga hasko mata lokacin baya.
Watarana da misalin ƙarfe sha daya na dare ta shigo gidansu cikin hanzari, ta wuce makwancinta, abu kawai ta ɗauka cikin sauri, ta kama hanya za ta fita kenan, ta jiyo muryar Innarta daga bayanta "Luba ina kuma za ki? Duk yinin da kika yi a waje bai ishe ki ba, sai kin koma kin kwana?" Cikin damuwa Innar tata ke magana.
Da yake a lokacin ta riga ta fanɗare, wani uban tsaki ta ja tare da juyowa a fusace "Gaskiya Inna kina da matsala! Kin cika sa'ido, wannan fa rayuwata ce ba taki ba." Tana gama faɗa ta yi gaba abunta, ba ta ko damu da halin da Innar zata shiga ciki ba.
Tana kai nan a tunaninta ta ja dogon numfashi, ta sani ta saka iyayenta kuka da yawa a wani shuɗaɗɗen zamani, yau kuma ga shi nata ƴaƴan suna saka ta hawaye.
Da za a iya maido da hannun agogo baya, da ta ta tariyo rayuwarta ta baya ta shafe manyan kura-kuranta, ko don ƴaƴanta a yau su zama shiryayyu.
A can ƙofar ɗakinsu Hanifa kuwa Mankas ne a tsaye yana rangaji yana jiran Hanee ta miƙo masa alƙawarinsa ya ta fi. "Yaya Mankas ka bari mana har ajima na baka." Ta faɗa daga cikin ɗakin.
Ko da Mankas ya ji haka ya ce "Tab! Ai ba zai yiwu ba, yarinya ki ban salalata yanzu ko na je na sami Baba in faɗa masa......."
"Yi shiru haka don Allah gani nan zuwa." Ta katse masa zance da wannan maganar.
Girgiza kai Sofi ta yi tare da faɗar "Koma meye ake ɓoye mana idan ta yi tsami ma ji."
Hanee bata tamkata ba sai wani uban tsaki da ta ja,tare da maka mata harara, sannan ta nufi ma'ajiyar kayanta ta lalubo masa wasu 'yan canji ta miƙa masa.
Ya karɓa yasa aljihu yana 'yar dariya ya ce "Ah to! Yarinya kin ga yanda ake, in dai zamu dinga yin haka dake to ki yi komai kike so zan rufa......"
Da sauri ta tarye shi da faɗar "An ji don Allah tafi haka." Gudun kada ya yi mata ɓaram-ɓarama.
"To ai hikenan." Ya faɗa tare da sa kai ya fice daga gidan.
Tana ganin ficewarsa ta sauke ajiyar zuciya "hmmmm!"
A ranta ta ce "Allah ya taimake ni, na samu na rabuda ƙaya. Amma dole in san yanda zan yi mu rabu da Mankas kafin ya jiƙa mun aiki....."
Ƙwafa ta yi ta juya ciki.
Ɓangaren Sofi kuwa tunanin gayen nan da suka ci karo da shi ne ya addabeta, sai tunani take.
Zuciyarta take bata wata shawarar, hakan ya saka ta yanke a ranta cewa zuwa gobe za ta fita da wuri don fara aiwatar da tunaninta.
Da misalin ƙarfe goma na dare alert ya shigo wayar Hanee Baby, Alhajinta ne ya turo mata kuɗi dubu ashirin.
Murmushi ne ya bayyana a fuskarta, a ranta take cewa "Daɗina da Alhaji kenan, baya wasa da alƙawari."
Kafin ta fita daga cikin saƙon ta ji ƙarar wani text ya shigo wayar.
Da sauri ta fita daga wanda take ciki ta duba sabon, yanzun ma text ɗinsa ne ga abinda ke rubuce "Hanee Baby ga kuɗin jinyar nan, kamar yanda na alƙawarta, ki kula mun da kanki. Na ga alamar akwai wanda kike wa ɓoyon kurwa a kusa. Idan kin samu sarari ki kira ni."
Wani ƙayataccen murmushi ta yi sannan ta masa reply na godiya, danna power wayar ta yi tare da koma kwanciya ta faɗa kogin tunanina.
Fatanta da duk burinta bai wuce ta samu lafiya ba da gaggawa domin ta ci gaba da sharholiyarta, Allah ya gani kwana biyun nan da bata fita ba duk a tauye take jin kanta, ga shi kwabon Kowa ya daina shigo ta, 'yar sana'ar da take ta kawar da hankalin mutane ma, kwana biyu bata yi ba, saboda ba lafiya.
Tunanin take taya zata iya kashe wannan kuɗin da Alhaji ya turo mata ba tare da an tuhume ta a gida ba?
Washegarin ranar da misalin ƙarfe sha biyu na rana Sofi ta yo wanka, sannan ta shirya a cikin atamfa riga da siket da suka ɗame ta.
Ba ta yi wata doguwar kwalliya ba, hoda kawai ta shafa sai ɗan man leɓe, amma fuskarta ta ɗan yi ma'ana duk da cewa ba wata kyakkyawa ba ce, sannan ita ba fara ba ce, haka nan kuma ba baka ba ce, sai dai a kirata da chocolate colour.
Har yanzu kana iya ganin sauran mikin a gaban goshinta.
Wani yalolon ƙaramin mayafinta ta ɗauko, da ganinsa kasan ya ɗan kwana biyu, yana riƙe a hannunta ta fito zuwa ɗakin Inna, lokacin fitar Baba kenan daga gidan, tun da dama can shi ba aikin fari ba na baƙi, kawai yana zaman jiran na Allah ne.
Ba ko sallama ta faɗa ɗakin, Inna tana zaune akan yagaggiyar ledar ɗakin da ta gama yin ƙura, akanta ta tsaya ƙerere ta ce "Inna ni zan fita."
Da mamaki Innar ta ɗago kanta ta sauke dubanta kan fuskar Sofi "zuwa ina kuma Safiya? Shin ko kin manta baki da lafiya ne?"
Ɗauke kai Sofin ta yi tare da juyawa ta fara tafiya tana faɗar "Ni nasan inda za ni Inna, kuma karki damu da ni ai na ji sauƙi."
Innar bata kuma cewa ƙala ba, sai sake baki da ta yi galala.
Har Sofi ta kai Ƙofa ta ci burki ba tare da ta juyo ba ta ce "Inna ki mun addu'a, Allah ya sa na dace da samun abinda zan fita nema, domin kuwa in har na rasa wannan damar akwai matsala."
Daga haka ta ƙarasa ficewa daga ɗakin kana ta bar gidan gaba ɗaya.
Tafe take tana ta famar sauri tare da addu'ar Allah ya saka ko labarinsa ta samu a gun.
Ta zo wucewa ta wajen Magama Uku ta hango Sakina tsaye akan ɗaya daga cikin layuka ukun ita da wani saurayi, suna tsaye daf da juna, kai da ganin gayen kasan irin tsagerun yarannan ne da iyayensu suka sallamawa duniya su.
Ɗauke kai ta yi kamar ba ta gan su ba ta bi ɗayan layin ta wuce tana girgiza kai.
Tsaki ta ja "mtssw" a ranta ta ce "Allah ya waddan naka ya lalace, dama haka duniya take matuƙar ba zaka iya kame bakinka daga aibata wasu ba, to abun kan iya komawa kan yayanka. Nan ba zagin da Iya mai bakin Aku bata mana, ashe mai bunu a gindi ne ke kai gudunmuwar gobara."
Wani tsakin ta kuma ja tare da ƙara saurin tafiyarta.
A gida kuwa, ko da Hanee ta tabbatar da ficewar ƙanwar Tata, ga shi Maryam tana Makarantar boko ba kowa a ɗakin sai ita kaɗai.
Da sauri ta buɗe idonta tare da tashi zaune ta janyo wayarta tana murmushi cikin nishaɗi ta ce "Bari in yi amfani da wannan damar na rage zafi."
Alhaji Saminu ta dannawa kira, har kiran ya yanke bai ɗaga ba, tana ƙoƙarin sake kiran shi ne kiransa ya shigo wayarta.
Faɗaɗa murmushinta ta yi sannan ta yi gyaran murya, cikin zaƙuwa ta ɗauka.
Daga can ɓangaren Alhaji ne ya fara magana kamar haka "Hanee Baby! Ya, kin saku kenan?"
Cikin wata iriyar murya mai sanyi ta ce "eh Alhajina kwana biyu, jikina da Ruhina sun raunata sosai."
Murmushi mai sauti ya yi kana ya ce "to ya jikin?"
"Ba sauƙi." Ta amsa a wasance.
"Subhanallah! Menene ya raunatawa Babyn Ruhi da gangar jiki?"
Ƙara rage sautin muryarta ta yi sannan ta ce "Jikina ya raunata ne a dalilin ciwon da ke cinsa, amma shi Ruhina rauninsa ya samu ne a dalilin nisanta da kai, ka ga kenan ta ya zance na ji sauƙi?"
Yar dariya ya yi cikin nishaɗi, sai yanzu ya fahimci inda ta dosa, 'Hanee Baby ba dai Jaraba ba?'
Ya faɗa a ransa.
Daga haka hirar ta su ta canza salo, zuwa gurɓatacciyyar hira, sun jima sosai kafin su kashe waya.
Kwanciya ta yi tana mayar da numfashi, sai murmushi take faman yi ita kaɗai "Shi ya sa nake mugun ji da kai Alhaji, ba dai iya soyayya ba, ga sake kuɗi."
A can layinsu Maheerah kuwa, Sofi ce tsaye a daidai gun da suka yi karo da gayen rannan, sai waige-waige take kamar zata gan shi.
Tunani ta hau yi, shin ta ina zata fara nemansa tunda ko sunansa bata sani ba?
"Ki je ki kwatantawa maishagon can sifarsa ko Allah ya sa ya san shi." Wani sashe na zuciyarta ya shawarce ta.
Bata musawa zuciyar tata babta matsa tare da tambayar Haliru Maishago, ko yasan wani gaye mai sifa kaza da kaza.
A take ya ce bai sani ba, bata haƙura ba, ta ci gaba da tambayar duk Namijin da ta gani, bata samu amsa ba.
Har ta gaji ta sare, ta kuma cire rai daga tunanin wannan dabarar zata fisshe ta, don haka ta yanke hukuncin komawa gida domin ta sake sabon shirin nemansa, domin ta yiwa kanta alƙawarin duk rintsi duk wuya sai ta nemo shi, haka kuma sai ta mallake shi. (Ku ji mun jaraba daga ganin mutum rana ɗaya sai ki kwallafa rai a kansa?)
Har zata juya ta tafi kamar ance ɗago kanki, ta hango shi yana tahowa fuskar nan a haɗe kamar dai waccan ranar.
Murmushi ta saki a ranta ta ce "Shi dai wannan mutumin kullum fuska a tamke, kamar wanda aka aikowa saƙon mutuwa."
Tana nan tsaye tana wannan tunanin bata ankara ba har ya zo ya gota ta.
Cikin sauri ta sha gabansa tana faɗar "Mun sake haɗuwa My Man, ya kenan?"
Ƙanƙantar da idonsa ya yi yana kallonta, shi sai ma yanzu ya gane ta "Ke ce? Me na faɗa miki a ranar haɗuwarmu ta farko?" Ya faɗa a zafafe.
Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Kamar cewa ka yi kar na sake mu sake haɗuwa domin......
Ko da yake na manta sauran idan na tuna na faɗa maka."
'Kut lallai wannan ta kai yar rainin wayo wallahi.' ya faɗa a ransa.
A zahiri kuwa ƙara haɗe fuska ya yi ya ce "Kauce mun daga hanya."
"Saboda me?" Ta tambaya.
'Lallai wannan ta cika neman magana, da gani ba natsattsiya ba ce' ya kuma faɗa a ransa.
A zahiri kuma cewa ya yi "Saboda bana son ganinki."
Daga haka ya matsa ta gefenta ya wuce yana huci, domin ta ƙara rura masa wutar da ke ci a ransa. Bata bar shi da zafin cin fuskar da masoyiyarsa ta masa ba, tana neman ƙarasa shi. Shin ita wacece?
Da wannan tunanin ya shige motarsa ya fige ta da ƙarfi.
Tana ganin wucewarsa, cikin hanzari ta ƙarasa gun Haliru Maishago ta ce "Malam ai ka ga wanda mu ka gama magana da shi yanzu ko? To shi nake tambayarka, ka san shi?."
Ta inda ya bi ya wuce Haliru ya bi da kallo kafin ya mai da dubansa kanta ya ce "Me yasa kike tambaya a kansa?"
Ba kunya ta ce "Ka sani ko ina son shi ne?"
Murmushin takaici ya yi sannan ya ce "Yarinya dama kin haƙura da wannan zancen domin......."
Ko me Haliru maishago zai sanarwa Sofi?
Ku tara da ni a shafi na gaba.