Gwamnatin Neja ta dora alhakin sace ɗalibai kan sakacin makarantar  B St. Mary

Gwamnatin Neja ta dora alhakin sace ɗalibai kan sakacin makarantar  B St. Mary

Gwamnatin Jihar Neja ta dora alhakin sace ɗalibai da malamai daga Makarantar St. Mary’s Catholic School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara, kan kin bin umarnin tsaro da aka bayar tun da farko.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Abubakar Usman, ya fitar, gwamnati ta ce lamarin “abin takaici ne kuma za a iya kaucewa,” domin bayanan sirri sun riga sun nuna yiwuwar kai hari a yankin Neja ta Arewa.

Gwamnati ta bayyana cewa ta ba da umarnin rufe makarantu  a yankin, amma St. Mary’s ta sake bude makarantar ba tare da neman izini ko sanar da hukuma ba.

Hukumomin tsaro na ci gaba da tantance adadin waɗanda aka sace a harin da ya faru tsakanin ƙarfe 2 zuwa 3 na safe a ranar Juma’a.

An fara aikin ceto, kuma gwamnati ta ce tana aiki tare da jami’an tsaro don ganin an kubutar da dukkan waɗanda aka sace.

Gwamnatin ta yi kira ga makarantu da shugabannin al’umma da su bi shawarwarin tsaro, tana mai cewa tsaron ɗalibai shi ne babban fifiko.