A kowane Yanki Ka Fito A Nijeriya Za Ka Iya Neman Shugaban Ƙasa a 2023----PDP
A taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a hidikwatar Jam'iyyar PDP ta ƙasa, zaman ya amince takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jamiyyar ya zama a buɗe ga kowa da kowa ba tare da la'akari da yanki ba.
Wannan batu ya kawo ƙarshen raɗe-radɗn da ake yi cewar takarar shugaban ƙasa za ta koma kudu, bayan da aka amince cewar shugaban jamiyyar na gaba da za a zaɓa nan gaba a karshen watan nan, zai fito ne daga yankin Arewacin Najeriya.
Jam'iyar ta aminta da soke Karɓa-karba a fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 abin da ake gani zai taimaki jam'iyar a kakar zaɓe mai zuwa.
Manyan 'yan takara daga Aewa za su ɗaura ɗamara na ganin sun samu damar tsayawa jam'iyar takara a zaɓen 2023.