Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara Ta Kuɓutar da  Mutane 187, Da Aka Yi Garkuwa Da Su 

 Jami'an 'yan sanda na hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar shiga  dajin Tsibiri a karamar hukumar Maradun, inda sakayi  nasarar ceto mutane 187 da aka sace a kauyen Rini na karamar hukumar Bakura, kauyen Gora na karamar hukumar Maradun, Sabon Birni da Shinkafi a karamar hukumar Shinkafi. 

Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara Ta Kuɓutar da  Mutane 187, Da Aka Yi Garkuwa Da Su 
Waɗanda aka ceto kenan suna cikin wani hali

 Daga Aminu Abdullahi  Gusau.

 Biyowa bayan aiwatar da sabbin matakan tsaro da gwamnatin jihar Zamfara, da  'yan sanda da sauran hukumomin tsaro na kai hare -hare  wuraren da aka gano maboyar  yan bindiga ne  a sassa daban -daban na jihar domin dakile miyagun ayukan su,  kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.

 Jami'an 'yan sanda na hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar shiga  dajin Tsibiri a karamar hukumar Maradun, inda sakayi  nasarar ceto mutane 187 da aka sace a kauyen Rini na karamar hukumar Bakura, kauyen Gora na karamar hukumar Maradun, Sabon Birni da Shinkafi a karamar hukumar Shinkafi. 

 A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar SP Muhammed Shehu, ya ce wadanda aka sace wadanda suka kwashe makwanni da dama a tsare an ceto su ba tare da wani sharadi ba.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba N Elkanah yayin mika wadanda aka ceto ga wakilin Gwamna Mohammed Bello Matawalle da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Kabiru Balarabe Sardaunan Dan Isa ya ce, sabbin matakan tsaro a jihar  yana haifar da sakamako mai yawa, saboda hakan ya haifar da nasarar ceto mutane da yawa da aka sace  kuma aka haɗa su da danginsu.

 Hakazalika, an cafke 'yan fashi da abokan aikin su, masu basu bayanan sirri, an kuma  gurfanar da wasu a gaban kotu yayin da ake  gudanar da bincike akan sauran da aka kama. a ofishin yan sandan dake Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

 Kwamishinan ya  ba da tabbacin cewa, 'Yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu don tabbatar da dawowar dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar.

  Ya jajantawa wadanda abin ya rutsa da su kan wahalar da suka sha yayin da suke tsare kuma ya yi alkawarin cewa 'yan sanda za su rubanya himmarsu don kare rayuka da dukiyoyin jama'ar  jihar Zamfara.

Da yake karbar mutanen da aka kubutar, wakilin Gwamna Matawalle ya gode wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro kan juriya da aiki tukuru wajen aiwatar da sabbin matakan tsaro, sannan ya ba su tabbacin gwamnatin jihar na ci gaba da ba su goyon baya da karfafa gwiwa don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

 Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar za ta tabbatar da cewa an ba  wadanda abin ya shafa kulawa mai kyau kafin a  sada su  da iyalansu.