Dalilin da ya sa babu wani gwamna da ba zai yi Tinubu a 2027 ba - Uba Sani
Dalilin da ya sa babu wani gwamna da ba zai yi Tinubu a 2027 ba - Uba Sani
Uba Sani, gwamnan jihar Kaduna, ya ce abu ne mai wuya a samu wani gwamna a Najeriya da zai kalubalanci sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a wajen bude taron tattaunawa na kwana biyu tsakanin gwamnati da al'umma, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House, Kaduna.
Ya ce: “Baya ga haka, babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da ya ba gwamnonin jihohi da gwamnatocin jihohi goyon baya kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a yanzu.”
“Sakamakon haka, da wuya a samu wani gwamna a Najeriya da zai tsaya ya kalubalanci shugaban kasa.”
managarciya