Mamallakin Jaridar Blueprint Ya Zama Dan Takarar Gwamna A Neja
Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna
Bayan zaben fidda gwani na kujerar gwamnan Neja da jam'iyyar NNPP ta gudanar wanda ya baiwa Alhaji Ibrahim Yahaya Muhammed Sokodoke nasarar da ya janyo cecekuce da rubuta korofe korofe ga sauran abokan takararsa, uwar jam'iyyar ta bukaci sake sabon zabe kamar yadda sakataren tsare tsare na jam'iyyar a jihar Neja, Mista Anthony Frances ya bayyanawa manema labarai a sakatariyar jam'iyyar da ke Minna.
Frances yace lallai mun gudanar da zaben fidda gwani tsakanin mutane uku kuma korafe korafe sun taso da ya kai ga kafa kwamitin da zai dubi koke koken masu koken, kuma ya kammala aikinsa, yau alhamis bisa amincewar hukumar zabe ta kasa an ba mu damar sake wannan zaben, cikin ikon Allah kamar yadda wanda ya jagoranci zaben, Dakta Mukhtar Bala ya bayyana maku an yi zabe wanda dalaget 124 cikin 125 da aka tantance suka jefa kuri'a.
Zaben dai an gudanar da shi bisa kulawar tsattsauran kulawar jami'an tsaro, inda dalaget 124 cikin 125 da akan tantance suka jefa kuri'arsu.
Alhaji Muhammad Idris Malagi ( Kakakin Nupe) mamallakin jaridar Blueprint ne ya samu nasarar zaben.
Jami'an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da suka sanya idanu a zaben sune Bashira I. Abdussalam da Zubairu Bala Usman a matsayin mai taimaka ma ta.
Tunda farko dai yayan jam'iyyar na NNPP sun nuna rashin gamsuwarsu da zaben fidda gwani karo na farko, wanda yasa tun bayan kammala zaben fidda gwanin da ya baiwa Sokodoke nasara, karbuwar jam'iyyar ya fara baya a wajen magoya bayan jam'iyyar.
Samun nasarar Idris Malagi da ake tsammanin yana da goyon bayan masu fada aji a siyasar jihar, musamman tun bayan faduwarsa zaben fidda gwani a jam'iyyar APC da ya kai ga dubban magoya bayansa na kiran da ya canja sheka zuwa wata jam'iyyar ta yadda siyasar jihar za ta iya samun daidaito.
Da yake karin haske ga jaridar Managarciyya, shugaban jam'iyyar APGA, Malam Musa Aliyu, yace maganar cewar akwai dokar da ta hana mutum idan ya tsaya takara a wata jam'iyya kuma ba a yi masa adalci ba, bai da ikon komawa wata jam'iyyar ba gaskiya ba ne.
Kasancewarsa dan jiha da ke son taka rawa a siyasar jihar yana da damar zuwa duk jam'iyyar da yaso dokar zabe bai hana shi ba.
Ban tafi wajen zaben ba, amma jagorancin gamayyar jam'iyyun siyasar a jiha, bisa jagorancin Alhaji Isah Bello Maikujeri ta halarci wajen kuma ta yaba da yadda zaben ya gudana.
managarciya