A Hukumance APC Ta Aikawa Hukunar Zaɓe Ranar Da Za Ta Yi Babban Taronta Na Ƙasa
Jam'iyar APC ƙarƙashin Shugaban Riƙo kuma Gwamnan Yobe Alhaji Mai Mala Buni ta bayyana aike da saƙon takarada zuwa ga hukumar zaɓe (INEC) domin Shelantama hukumar cewa "Jam'iyar ta APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa, inda zata gudanar da zaben shugabannin Jam'iyar na ƙasa".
Jam'iyar ta aike da Takarda a yau Alhamis 03/02/2022 zuwa ga Hukumar Zabe mai zaman kanta mai ɗauke da sa hannun Shugaban riƙo Gwamnan Yobe dakuma Sakataren riƙon Jam'iyar na Ƙasa Hon. John James Akpanudoedehe a cikin Takarda mai Lamba "APC /NHDQ/INEC/19/021/40.
Wannan ya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa cewar akwai yiwuwar jam'iyar ta ɗage taron zuwa wani wata na daban.
ABUBAKAR S. LIMANCHI.
(Sarkin yaƙin Shehi)
On new Media
managarciya