2023: Mutanen Nijeriya da kudin su za su talllafawa Tinubu ya ci Zabe-- Hon. Ibrahim Adamu Tiga

2023: Mutanen Nijeriya da kudin su za su talllafawa Tinubu ya ci Zabe-- Hon. Ibrahim Adamu Tiga

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

 

Mai baiwa shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA shawara wato  SSA motor Park  Hon. Ibrahim Adamu Tiga ya bayyana cewa yana da yakini cewa alummar  Nigeriya za su zabi dan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinibu da Kashin Shatima da ake sa ran Isowa Kano yau da a misalin 11: 00 na safe,

 
Ya kara da cewa ba za ka taba hada nagarAtiku da tinibu ba yana Mai cewa Atiku ya rike mataimakin shugaban kasa amma haryar da ta tashi daga Gombe zuwa Yola Atiku ya kasa gyarawa, don haka ya ce ko wannan rashin gyaran hanyar da bai yi ba, dalilin ne da yan Nigeriya za su ki yi,  saboda ba yi kishi ba,
 
A matakin Gwamnatin tarayya kuwa Hon. ya bayyana Asiwaju Bola Ahmad Tinibu da cewa: "lallai shi ne wanda ya dace ya Shugabanci kasar Najeriya; duba da kokarinsa na ganin cewar talakawa sun amfana da mulkin dimokradiyya.
 
Hon. Tiga ya kuma ce: "lallai a jihar Kano ba wanda ya dace ya zama Gwamna a bayan Ganduje in ba Gawuna da mataimakinsa Murtala Sule Garo ba,  domin cancanta da kuma zage dantsensu na ganin ci gaban mutanen Kano ba, ya bunkasa, bugu da kari kuma su din matasa ne masu jini a jika."
 
Hon. ya kuma ja hankalin yayan  jam'iyyar APC da su hade kansu; kana su bada hadin kai don ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a Mataki na Kano da ma kasa baki daya.
 
Tsohon dan Takarar Majalisar jihar ya yi kira ga al'umma da su fito kwansu da kwarkwatarsu su don tarbar mai girma Tinubu.