2027: Bajare ne za mu tura ya waƙilce mu a majalisar wakilan Nijeriya----Matasa

2027: Bajare ne za mu tura ya waƙilce mu a majalisar wakilan Nijeriya----Matasa

Matasa a kananan hukumomin Sakkwato ta Arewa da ta Kudu sun fara kira ga Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare da ya fito takarar dan majalisar wakilan Nijeriya don ya waƙilce su.
A hirar da wakilinmu ya yi da matasan sun nuna Bajare ne kadai za su zaba a kakar zabe mai zuwa ta 2027 don shi ne mai kishinsu.
Muhammad Auwal dake unguwar Marina ya bayyana cewa Bajare ne za mu tura ya waƙilce mu a majalisar wakilan Nijeriya domin shi ne zai iya kawo cigaba da ake bukata.
"A matsayin sa wanda ya san majalisa ciki da bayanta in ka tura shi ya waƙilce ka zai kawo maka romon dimukuradiyya don shi ya yi an gani, mutum ne haziki."
Kabiru Gandu ya ce yankinsu na buƙatar wakilcin Bajare domin salon kawo sauyi irin nasa daban ne duk wanda yasan abin da yake yi, na bukatar sa a harakar jagoranci.
Karima Gidan Dare ta ce mu mata mun san irin karimci na Bajare tun sanda ya raba tufafin makaranta da littafai ga yara har yanzu ba a samu wani dan majalisa da ya yi irin haka ba.
"Ya ba da gudunmawa ga harkar cigaban ilimi a jiha musamman bangaren mata jajircewarsa ne ta kara kawo cigaban ilmin mata a jihar nan ta Sakkwato."