Kashi 70 abokan siyasa ta sun barni---Bafarawa

Kashi 70 abokan siyasa ta sun barni---Bafarawa

Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya koka kan yadda abokan siyasarsa suka bar goyon bayansa bayan daukar dogon lokaci ana tare cikin gwagarmaya.
Tsohon Gwamnan a lokacin da yake jawabi ga wasu matasa magoya bayansa da suka kai masa ziyara a gidansa dake Sakkwato ya ce "Kashi 60 ko  70 na abokan siyasa ta sun barni, in na ce bari na watsar da komai na tafiya ban kyauta ba dalili kuwa ana bukatar shugaba da jajircewa."
Ya ce duk wanda ya damu da halin jama'a ba ya da wurin hutawa, yanzu yaran da aka bari ba karatun addini bana boko in sun girma ya za a yi da su, an koro na kauye ba noma.
"Yau shekara 18 na bar Gwamnati ban taba zuwa ofis ko gida na kowa ba neman bukata, duk wanda kuka kawo(matasa) shi ne zanbi a dukkan kujerun siyasa, jihadi ne don ceton kanmu."
Ya baiwa matasa shawara da su hada kansu kar su bari a saye su don samar da cigaba a jiha da kasa baki daya.