Matasa  Ku Tashi Tsaye A Dama Da Ku A Siyasar 2023----Shugaban PDP

Matasa  Ku Tashi Tsaye A Dama Da Ku A Siyasar 2023----Shugaban PDP

Matasa  Ku Tashi Tsaye A Dama Da Ku A Siyasar 2023----Shugaban PDP

 Shugaban Jam'iyar adawa ta PDP mai jiran gado, Dakta Iyorchia Ayu ya yi kira ga matasan Nijeriya da su tashi tsaye su nemi madafan iko a kowanne matakai na siyasa a shekarar zaɓe ta 2023.

Ayu ya kuma yi wa matasa ƙaimi da cewa kar su bari su zauna su na jira har sai wani lokaci a ce su zo su ɗana mulki, inda ya ce su tashi tsaye a dama da su domin ba a samun mulki a ɓagas.

Shugaban ya yi wannan kira ne a ƙarshen mako lokacin da wata ƙungiyar matasan Jihar Benuwe su ka kai masa ziyara a gidansa da ke Maitama, Abuja.

Ayu, tsohon shugaban majalisar dattijai ya shawarci matasa da su sa ƙarfin su a inda ya dace, in da ya ce "makoma ta matasa ce, amma fa ga waɗanda su ka zaɓi hakan."

"Mun daɗe mu na ji a na cewa "yara manyan gobe" amma mu har yanzu ba mu gani a ƙasa ba. Tabbas makoma ta matasa ce amma fa wadanda su ka yarda da hakan, su ka yi aiki kan cimma manufa mai kyau, su ka kuma bi hanya mai kyau wacce su ka ga ta fi musu.

"Ba magana a ke yi ta matasa ƴan ƙwaya, karuwai da ƴan ta'adda da kuma ƴan yahu-yahu ba. Wasu ma runduna su ka kafa ta ta'addanci, to irin waɗannan matasan ba su da makoma mai kyau.

"Ku haɗa kan ku, ku tafi a ƙungiyance ku nemi abinda ku ke so, har da ma madafan iko.

"Mu tun muna ƙanana mu ka samu nasarori a rayuwarmu. Na gama jami'a ina da shekara 23, na samu digiri na na uku a shekara 31 na zama babban mai koyarwa a jami'a ina da shekara 37, an zabe ni a sanata ina da shekara 39 sannan abokan aiki na su ka zaɓe ni shugaban majalisar dattijai ina da shekara 40. Sabo da haka ku dage sosai ku ginawa kan ku rayuwa mai kyau mai amfani," in ji Ayu.

Daily Nigerian Hausa