2023:Gwamnonin PDP Sun Fara Yunƙurin Tsayar Da Ɗaya Daga Cikinsu Takararar Shugaban ƙasa
Yunƙurin nason kawo ƙarshe ƙudirin manyan 'yan siyasar nan guda uku da ke son yin takara a 2023 cikin jam'iyar PDP Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Rabiu Musa Kwankwaso. A zaɓen da aka gudanar gwamnoni sun nuna karfin da suke da shi in da suka karɓe manyan muƙaman jam'iyya, in da gwamnan Benue Samuel Ortom ya bayar da shugaban jam'iyya na ƙasa Iyorchia Ayu, gwamnan Oyo Seyi Makinde ya bayarda mataimakin shugaba na kudu Taofeek
2023:Gwamnonin PDP Sun Fara Yunƙurin Tsayar Da Ɗaya Daga Cikinsu Takararar Shugaban ƙasa
Bayan kammala babban taron shugabanin jam'iyar PDPna ƙasa gwamnoni a jam'iyar sun fara yunƙurin tsayar da ɗaya daga cikinsu babu hamayya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.
Yunƙurin nason kawo ƙarshe ƙudirin manyan 'yan siyasar nan guda uku da ke son yin takara a 2023 cikin jam'iyar PDP Atiku Abubakar, Bukola Saraki da Rabiu Musa Kwankwaso.
A zaɓen da aka gudanar gwamnoni sun nuna karfin da suke da shi in da suka karɓe manyan muƙaman jam'iyya, in da gwamnan Benue Samuel Ortom ya bayar da shugaban jam'iyya na ƙasa Iyorchia Ayu, gwamnan Oyo Seyi Makinde ya bayarda mataimakin shugaba na kudu Taofeek Arapaja, sai gwamnan Rivers Nyesom Wike ya kawo sakataren jam'iyya na ƙasa Sanata Samuel Anyanwu, Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da Skataren tsare-tsare Umar Bature.
Gwamnonin suna yunƙurin tsayar da ɗaya daga cikinsu, ƙungiyar gwamnoni tana da ƙarfin da za ta iya zaɓar wanda suka ga ya dace.
Wata majiyar ta ce gwamnonin su 13 da suka karɓe tafiyar jam'iyar PDP haka suna son kawo wanda zai yi takarar mataimakin shugaban ƙasa da kansu gaba ɗaya.
Wannnan yunƙurin nasu wata koma baya ce ga takarar Atiku, Kwankwaso da Saraki a cikin jam'iyar.
managarciya